Dara ta ci gida; Ƴan sanda sun kama kwamandan Hisbah na Kano a otal tare da matar aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta tabbatar da labarin kama ɗaya daga cikin manyan jami’an ta mai suna Sani Nasidi Uba Remo da ƴan sanda suka yi a Otel a Nomansland dake Unguwar Sabon Gari, bisa zargin yana tare da wata matar aure.


Majiyarmu ta jaridar Sahelian ta ta yanar gizo ta ruwaito samun rahoto daga wata majiya mai tushe daga rundunar ‘yan sanda ta Unguwar Nomansland, inda ta sanar da ita cewa sun cafke Remo ne bayan sun samu korafi daga mijin matar. Kuma an kama Remo da matar a ɗakin otal din dake Sabongari.

Wani Mataimakin Kwamandan Hisbah ya je ofishin ’yan sandan don neman an bayar da belin kwamandan da aka kama, wanda da farko’ yan sanda suka yi watsi da buƙatar kafin daga bisani suka mayar da ƙarar zuwa hedkwatar Hisbah don ci gaba da gudanar da bincike.

A nasa bangare, Babban Kwamandan Hisbah na Kano, Sheikh Muhammad Haroun Ibn Sina, ya tabbatar da cewa sun kaɗu da samun labarin. Amma, ya bayyana cewa, ya kafa kwamiti da zai binciki lamarin tare da miƙa masa rahoton binciken nan da kwanaki uku kafin ɗaukar matakin da ya dace.

Sani Remo dai ya kasance babban jami’i mai kula da sashen kama karuwai kafin a mayar da shi sashin hana bara na rundunar a cewar majiyarmu ta Sahelian.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment