MAULIDIN FARIN JAKADA/ SALEH KAURA

MAULIDIN FARIN JAKADA.. ( 01 )

TARIHIN ABIN TINKAHON TALIKAI…

Shi ne: Abul Kasim, Muhammad (SallalLahu alaiHi wa aliHi wa sallam) [53 KH- 11 BH/ 571-633 MLD], dan Abdullahi [81 KH- 53 KH/ 544-571 MLD], dan Abdul-Mutallab [127 KH- 45KH/ 500- 579 MLD], dan Hashim.

Bakuraishe, dangantakarsa tana haduwa da Adnan, cikin ‘ya’yan Annabi Isma’il dan Annabi Ibrahim al-Khalil (Alaihima as-salam).


Mahaifiyarsa ita ce: Sayyida Aminatu ‘yar Wahab [45 KH-/ 575 MLD], Bakuraishiya, daga dangin Zuhra.

An haife shi a garin Makka, ranar litini [19 ga watan Rabi’u al-Awwal, shekara ta 53 KH/ 20 Afrilu, shekara ta 571MLD], amma mafi shahara shi ne an haife shi ne a rana 12 ga watan Rabi’ul Awwal.

Halimatu al-Sa’adiyya ce ta shayar da shi a kauye, ita ‘yar kabilar Bani Sa’ad ibn Bakr ibn Hawzan ce.

Ya tashi maraya ne, domin mahaifinsa ya rasu tun kafin a haife shi, sai mahaifiyarsa ta dauki nauyin kula da shi har zuwa lokacin da ta rasu, lokacin yana dan shekara shida a duniya, sai kakansa Abdul-Mutallab ya raine shi, har zuwa lokacin da ya rasu -lokacin yana dan shekara takwas a duniya- sai baffansa Abu Talib [75 KH- 3BH/ 540-620MLD] ya raine shi.

Ya tashi yana mai cikakken hankali, mai himma da gaskiya da amana, ga gwarzanta da kyawawan dabi’u, abin da ya kai ga mutanensa sun yi masa lakabi da “al-Sadik al-Amin” (mai gaskiya da rikon amana).

Ya halarci yarjejeniya da aka sani da suna “Halfu al-Fudhul” da mutanen Makka suka yi domin taimakon wanda aka zalunta, da amsar ma masu rauni hakkokinsu daga masu karfi.

Ya yi kiwon tumaki na dan wani lokaci, sannan ya yi kasuwanci, ya tafi garin Sham domin yi wa al-Sayyida Khadija bint Khuwailid Ba’asadiya kuma Bakuraishiya [75 KH-3 BH /556-620MLD] kasuwanci.

Yana dan shekaru ashirin da biyar ne ya auri al-Sayyida Khadija, da ita ya haife dukan ‘ya’yansa -banda Ibrahim da ya rasu yana karami-, Ya zauna tare da matarsa ita daya (Khadija) bai kara aure ba har sai da ta rasu -yana dan shekara hamsin- a shekara [3 KH/ 620MLD]; daga nan ne ya yi auri sauran matansa, daya bayan daya.

Babu wanda ya rayu cikin ‘ya’yansa bayan wafatinsa sai ‘yarsa Sayyida Fatimatu [18 KH-11 BH/ 605- 632 MLD], wacce ta auri dan baffansa Sayyiduna Aliyu Ibn Abi Talib [23 KH- 40 BH/600- 661 MLD], tsatsonta ya cigaba ta hanyar ‘ya’yanta guda biyu: Sayyiduna al-Hasan ibn Aliyu [3- 50 BH/ 624- 670MLD] da Sayyiduna al-Husain ibn Aliyu [4-61 BH/ 625- 680MLD]… Sauran ‘ya’yansa da suka rasu tun yana raye su ne: al-Kasim, da Abdullahi, da Zainab, da Rukayya, da Ummu- Kulsum, da Ibrahim.

Bai taba bauta wa gunki ba tunda ya tashi, mutum ne mai yawan tunani da lura, yana mai binciken gaskiya, sannan ya fara kebe kansa a duk watan Ramadhan na kowace shekara, a kogon Hira, yana bautar Allah da tsari irin na abin da ya yi saura na Addinin da Annabi Ibrahim al-Khalil (Alaihis-salam) ya zo da shi.

Wata rana yana cikin kogon ne a watan Ramadhan na shekara [13 KH/ 610 MLD], wahayi ya zo masa daga Allah Madaukakin Sarki, inda ya zamo cikamakin Annabawa, kuma madawwamin sako, sai ya fara kiran makusantansa zuwa Musulunci a boye –na tsawon shekaru uku-, wasu mutane kadan suka yi imani da shi, sannan ya bayyana kira zuwa ga Musulunci.

Alkur’ani ya sauka masa a hankali- a hankali, masu rubuta wahayi kuma suna rubutawa, kana kuma suna haddacewa, shi ne mu’ujizar da ya kalu-balanci mutanensa da shi, da ma dukkan mutane da aljannu kan su zo wa wani abu da ya yi kama da shi.

Mushrikan Kuraishawa, da masu hannu da shunin cikinsu sun cutar da shi –shi da Sahabbansa-; sun kuma yi hakuri da juriya gami da jajircewa akan haka; Kuraishawa sun yi masu kawanya (sun hana su shige-da fice da hana a siyar masu, ko a saya daga gare su kamar yadda suka hana yin zumunci da su) a unguwar Bani Hashim har na tsawo shekaru uku, sun kusa su rasa rayuwarsu saboda yunwa, sai Ya yi wa wasu daga cikin sahabbansa –maza da mata- izinin yin hijira zuwa Habasha (Ethiopia) sau biyu, ya kuma fara gabatar da kansa da da’awarsa zuwa ga sauran kabilu; domin neman kariya da imani, da kuma keta wannan kawanya.
Lokacin da wasu jama’a (daga garin Yasriba) ‘yan kabilun al-Aus da al-Khazraj suka amsa kiran Musulunci, a shekara ta [2 KH], sannan suka dawo, bayan shekara daya [1 KH] ne su kulla yarjejeniyar kafa daular farko ta Musulunci –a garin Madina- a wani wuri da ake cewa da shi “al-Akba”. Sai sahabbansa suka fara yin hijira zuwa can.

Shi ma ya yi hijira tare da Sayyiduna Abubakar al-Siddik [51 KH- 13-BH/ 573-634 MLD] daga garin Makka zuwa Madina, ya shiga garin ranar litini [8 ga watan Rabi’u al’Awwal shekara ta 1 KH/ 20 ga watan Satumba shekata ta 622 MLD], sai ya gina Masallacin Annabi da yake Madina, ya kuma samar da farko kundin tsarin zamantakewa na farko a daular Musulunci.

Kuraishawa sun bi shi da kiyayya da ta’addanci har zuwa in da ya yi hijira; daga nan sai Allah Madaukakin Sarki ya yi masa izini shi da sahabbansa kan su yi yakin kare ‘yancin akida, da ‘yancin yin kira, da kuma kare garin Musulunci da daularsa: ((An yi izini ga wadanda ake yakarsu, kan su kare kansu, ganin cewa lallai an zalunce su, kuma lallai Allah mai iko ne akan taimakonsu. Su ne wadanda aka fitar da su daga gidajensu ba tare da wani dalili ba sai domin kawai sun ce Ubangijinmu shi ne Allah…)) [39-40, al-Haj]
Yakokinsa guda ashirin da takwas, ya yi su ne domin kare addini, da daula da kasa, da kuma ‘yanto yankin gabashin duniya daga mulkin mallakar Romawa da kama-karyarsu, da kuma haka ne Musulunci ya sami nasara akan shirka da bautar gumaka, da hadin-kan da Yahudawa suka yi da masu bautar gumaka; Larabawa suka hada-kansu a daular Musulunci –a karo na farko a tarihi-, jama’a gungu-gungu suka shiga cikin addinin Allah, kiran Musulunci ta fara ketare yankin tsibirin Larabawa zuwa makwabta, wadanda yake-yake suka rutsa da su –bayan wadannan nasarori- ba su wuce [386], su ne gaba dayan wadanda aka kashe cikin Musulmai da Mushrikai.

Aranar [20 ga wata Zul Ki’ida shekara ta 10 BH/ Fabrairu shekara ta 632 MLD] ya fita domin “Hajjatu al-Wa’da’i”, ya yi huduba mai tsawo a filin Arfa, a ciki ya ambaci dokokin hakkokin zamantakewa da na addini ga mutane baki dayansu, sannan ya dawo garin Madina al-Munawwara.

A ranar [28 ga watan Safar, shekara ta 11 BH/ Mayu shekara ta 632 MLD] Ya fara rashin lafiyar da ya yi sanadiyyar wafatinsa, ransa mai tsarki ya koma zuwa ga mahaliccinsa ne a [ranar lahadi 12 ga watan Rabi’I al-Awwal shekara 11 BH/ 7 Yuni shekara ta 632 MLD], bayan shekarunsa –a lissafin watan sama- sun kai [63] da kwanaki uku, a lissafin rana kuma [61] da kwanaki arba’in da takwas.

Wadanda suka shiryu zuwa Musulunci –lokacin da ya yi wafati- adadinsu ya kai [124,000] (dubu dari da ashirin da hudu), a lokacin adadin zababbu masana da suka jagoranci makarantar Annabta ya kai kimanin dubu takwas, mata a ciki sun fi dubu.

Kwararre wajen yin huduba, kalmominsa da Allah ya ba shi dauke suke da dimbin ma’anoni, idan yana huduba kan hana wani abu, ko yana gargadi idanuwansa sukan yi ja, yakan daga muryarsa, fushinsa yakan fito fili, kai ka ce yana gargadi a filin daga ne, idan kuma a filin yaki ne yake hudubar yakan dogara ne akan baka, idan kuma ba wurin yaki ba ne yakan dogara akan sanda.

Mutum ne mai dadin zance, yana da usulubi na yin magana dikin-dikin, kamar yadda yake da na yin sauri, idan yana magana yakan yi murmushi.

Ga tawali’u, yakan zauna ya ci abinci a kasa, yakan dinka tufafinsa da hannunsa, yakan gyara takalmansa da kansa, yakan yi wa iyalansa hidima ta gida, yakan amsa kiran talaka da bayi wajen samo masu abin da za su sa a bakin salati, yakan zauna tare da miskinai.

Yakan dauki lokaci yana zaune shiru, ba ya yawaita yin dariya, idan ma ya yi yakan sanya hannunsa ya rufe bakinsa, yakan yi ba’a kadan, amma duk abin da yake fadi gaskiya ne, idan ma ya yi ba’ar yakan dan rufe idanunsa.

Ga tsananin kunya, idan ya yi musafaha da wani ba ya fara janye hanunsa sai idan wanda ya gaisa da shin ya janye.

Kansa da hannayensa da kafafuwansa manya ne, shi ba dogo can ba, ba kuma gajere ba, fuskarsa tana da yalwa, gashinsa dogo har ya sauko, fuskarsa a kewaye, launinta ja-ja, gemunsa cike yake da gashi, bakinsa mayalwaci, yana da wushirya a hakoransa, idanuwansa bakake, yakan saki gashin kansa har zuwa wajen kunnuwansa, fitaccen launi ne da shi, kan kasusuwansa manya, yana sanya farar hula, yana shafa almiski a kansa da gemunsa, idan yana tafiya ba ya waige, idan ma zai waiga yana waiga wa ne gaba dayansa, tafiyarsa yana yi ne dai-dai, kai ka ce yana saukowa ne daga wuri mai tudu, idan ya sanya wani abu a gaba yakan yi yawan safan gemunsa.

Jarumi ne, ga gwarzanta, idan yaki ya yi yaki sahabansa sukan dogara da shi, idan abin ya yi tsananin yakan fi sahabbansa kusa da abokan gaba.

Yakan tsaya gaban Ubangijinsa yana “Kiyamul-laili” har kafafunsa su kumbura, mai tausayin mutane da dabbobi da tsirrai da ma abubuwan da ba su da rai.

Mai son duk wani abu mai kyau cikin halittun Allah, ba ya hana kansa jin dadin rayuwa da kayan kawanta.
Duk da cewa shi “Ma’asumi” ne (wand aba ya saba wa Allah) yakan yawaita yin shawara tare da sahabbansa, yakan kuma bi ra’ayin wadanda suka fi rinjaye koda kuwa ya saba da ra’ayinsa, idan ya yi nufin kai wani hari yakan rufe, ya yi kinaya da sabanin haka.

Ya sifanta kansa da cewa: ((Ubangiji na ya yi mani tarbiyya, ya kuma kyautata yi mini tarbiyyar)), matarsa A’ishat [9 KH- 58 BH/ 613-678 MLD] ta sifanta shi a inda take cewa: ((Gaba dayan dabi’unsa Alkur’ani ne)). Allah Madaukakin Sarki ya sifanta shi da cewa: ((Lallai kai din nan kana kan dabi’u ne masu girma)) [4, al-Kalam].

Allah Mai girma ya yi gaskiya, Allah ya yi tsira da aminci a gare shi, shi da mala’iku da muminai gaba daya har zuwa ranar sakamako.

Saleh Kaura

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment