Yadda Aka Kama Fatima Lauwali Da Albarusai 991 Zata Kai Ma Ƴan Bindiga A Zamfara

Yan sanda a Jihar Zamfara sun kama wata mata mai suna Fatima Lauwali, da albarusai 991 da take shirin kai wa wani kasurgumin dan bindiga a Jihar.



’Yan Sandan dai wadanda ke runduna ta musamman karkashin DSP Hussaini Gimba, sun kama matar ne mai kimanin shekara 30, bisa zarginta da yin safarar makamai ga ’yan bindigar da suka addabi jihohin Sakkwato, Zamfara, Katsina Kebbi, Kaduna da kuma Neja.

Da yake gabatar da matar ga ’yan jarida a Gusau ranar Juma’a, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ayuba Elkanah ya ce an kama ta ne a daidai wata gada da ke kan hanyar Sakkwato zuwa Gusau, babban birnin Jihar.

Matar dai, wacce ta amsa laifin da ake zarginta da aikatawa, ta ce ta jima tana yi wa ’yan bindigar yankin safarar makamai kafin dubunta ta cika.

A cewarta, “Ina kan hanyata ne daga kauyen Dabagi a Jihar Sakkwato, ina kokarin zuwa yankin Danjibga/Tsafe domin kai wadannan albarusan ne ga wani kasurgumin dan bindiga da ake kira da Adamu Alero.

“Shi ne dan bindigar da ya addabi Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara da wasu yankunan ma da dama na Jihar Katsina.

“Na yi nadama matuka da kamun da aka yi min, kuma ina neman afuwar mutanen da aka kashewa iyalai, musamman mata irina, da kananan yara, sanadin makaman da na yi safararsu,” inji ta.

Tun da farko dai, Kwamishinan ‘yan sandan ya ce a sakamakon titsiyen da aka yi wa wacce ake zargin, sun samu nasarar kai hare-hare maboyar ’yan bindiga a sassa da dama na Jihar.

“Mun yi musayar wuta da ’yan bindiga da dama, inda muka ji wa da yawa daga cikinsu munanan raunuka, wasu kuma suka tsere da raunin. Mun kuma kwace bindiga kirar AK-47, da wata bindigar dauke da alburusai 143,” inji Kwamishinan.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment