Ƙungiyar mai suna “ZAMFARA NEW MEDIA OPERATORS FORUM” (ZANMOF) an samar da kungiyar ne saboda inganta tare da tsaftace harkokin watsa labarai a yanar gizo. An kirkiro kungiyar ne saboda tsaftace harkokin yanar gizo ta fannin yada labarai musamman a kafafen sada zumunta domin yaki da kaucewa yada labarun karya wadan da ke kassara duniyar mu musamman kasar mu Najeriya.
Masu amfani da kafofin yanar gizo waje rubuce-rubuce da shafuka na gidajen jarida da na talabijin a yanar gizo a jihar Zamfara. A ranar Lahadi 21-03-2021 Sun yi zama na samar da wata kungiya wacce zasu dinga magana da yawu daya da aiki kafada da kafada a karkashinta domin cigaban al’ummar jihar Zamfara kwata.
Haka zalika an samar da kungiyar ne domin bam bance mutane masu zaman kansu a kafar yanar gizo wadan da ke da gidajen Jarida, da na talabijin da Rediyo, da mashahuran mawallafa, da sauran al’umma gama gari wadan da ke amfani da yanar gizo musamman a kafofin sada zumunta.
A zaman tattaunawar an samar da shuwagabanni na rikon kwarya na mutum shida wadan da za su ja ragamar kungiyar na wa’adin watanni shida.
An zabi;
Dr Anas Sani Anka, Shugaban Thunder Blowers, a matsayin shugaba (Chairman ).
Abdulmalik Saidu Maibiredi, Shugaban Mai Biredi TV, a matsayi Sakataren kungiyar, ( Secretary).
Abdulsamad Kabiru Musa, shugaban Jaridar Jekadiyar Zamfara a matsayin mai magana da yawun kungiyar (P. R. O).
Yusuf Hashimu Sani Shugaban Behsan TV a matsayin sakataren tsare-tsare ( Organizing Secretary).
Sai Masha hurin Dan jaridar nan kuma mawallafi Baba Halliru Andi a matsayin ma’ajin kungiyar (Treasure).
Rashida Haruna shugaban RH TV a matsayin Mai kula da walwalar Kungiyar (Welfare).
Haka zalika an kafa kwamiti kan tsara tsarin Mulki da dokoki, an ba wa kwamitin makwanni biyu aiki ya gabatar da daftarin rahoton a gaban kungiya don tattaunawa da amincewa.
A dayan bangaren kuma an sake kafa wani karamin kwamiti don tsara rijistar kungiya ta hukumar kula da harkokin kamfanoni da rijistar asusun a jiyar kudi.
📮 Abdulsamad Kabiru Musa State P.R.O ( ZANMOF)