‘Mun Kama Soja Dumu-Dumu Yana Ba ’Yan Ta’adda Kaki Da Albarusai’

‘Mun Kama Soja Dumu-Dumu Yana Ba ’Yan Ta’adda Kaki Da Albarusai’

Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi zargin cewa an kama wani jami’in soja tare da budurwarsa a kwanan nan bayan an same su da hannu dumu-dumu suna bayar da kakin sojoji da kuma albarusai ga ’yan bindiga a jihar.


Mataimkain Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Bashir Muhammad Maru ne ya tabbatar da hakan yayin wata zantawa da ’yan jarida ranar Juma’a, inda ya ce an sami nasarar ne sakamakon bayanan sirri daga mazauna gari.

“Yayin da gwamnati take jiran matakin da Rundunar Soja zata dauka akan wannan lamarin sannan ta fitar da matasayarta a hukumance, batun ya kara fito da maganar da Gwamna Matawalle ya sha yi a baya cewa matukar ba a kakkabe bata-gari da masu zagon kasa ba, ba lallai ne a cimma nasarar da ake sa ran gani a yaki da ’yan bindiga ba.

“Ina son yin amfani da wannan damar wajen jinjinawa mutumin da ya sami kwarin gwiwar zuwa ya fallasa wannan bayanin wanda ya kaimu ga kama wadanda ake zargin. Godiyarmu ba ta da iyaka,” inji shi.

Sai dai ya kuma karyata wasu rahotanni dake cewa an hallaka mutane 40 a wani hari da aka kai garin Tungar Baushe na jihar ranar Laraba

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment