An Sasanta Rikici Tsakanin Abdul’aziz Yari Da Kabiru Marafa

An Sasanta Rikici Tsakanin Abdul’aziz Yari Da Kabiru Marafa.



Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Gwamna Mai Mala Buni ya sasanta tsakanin tsohon gwamnan Zamafara, Abdul’aziz Yari, da tsohon Sanata, Kabiru Marafa da sauran masu ruwa da tsaki.

An gudanar da taron zaman lafiyar na awanni uku a sakatariyar jam’iyyar ta kasa a ranar Litinin.

Buni ya fadawa kafofin yada labarai cewa sasantawar ta kasance “gagarumar nasara”.Gwamnan na Yobe ya ce aikin da kwamitin nasa shi ne sake gina jam’iyyar a dukkan matakai da kuma hada kan mambobin kasar baki daya.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment