Ƴan Bindiga 6 A Zamfara Sun Mika Makamansu 14 Da Tarin Alburusai

A cigaba da yunkurinta na tabbatar da tsaron rayukka da dukiyoyin Al’umma
r Jihar Zamfara, Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun, a yau ta yi ta yi nasarar karbar tubabbun yan bindiga shida.

Lokacin Malamai ke yi wa Yan bindigar wa’azi da rantsar da su da Al-Qur’ani Mai Girma


Tubabbun yan Bindigar sun mika bindigogi 14 tare da Makamai daruruwan albarussai. A yayin karbar bindigogin gwamnatin Jihar Zamfara ta gayyato majalissar malamai ta Jihar wadanda su ka yi masu wa’azi akan muhimmancin zaman lafiya da kuma amfanin sulhu daga nan imam Malam Abubakar Fari, ya rantsar da su da alkur’ani mai girma akan na za su kara fashin daji, shaye-shaye, taimakawa masu aika-aika da duk wani aikin assha mai kama da haka.

Da ya ke jawabi mai daraja gwamnan Jihar Zamfara Hon Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun. Ya bayyana matukar jin dadinsa da wannan tuba da wadannan mutane suka yi. Daga nan ya yi kira ga sauran takwarorinsu da ke cikin dazukkan Jihar Zamfara, da su yi koyi da wadannan domin samun zaman lafiya a Jihar da ma kasa baki daya. Haka zalika Gwamnan ya Kara nanata matsayar gwamnatinsa na cigaba da karbar wadanda su ka yarda za su yi sulhun. Tare da yakar wadanda su ka ki mika wuya.

Rantsar da tsofaffin Yan Bindigar dai ya samu halar, dukkanin shuwagabannin rundunonin tsaro na Jihar Zamfara, Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Hon. Mukthar Anka, Sakataren gwamnatin Jihar Zamfara Hon. Bala Bello Maru, Shugaban Ma’aikatan Zamfara. Hon. Kabir Balarabe Sardaunan Dan’isa. Kwamishinoni, masu baiwa Gwamna shawara Malaman Addini da sauran muhimman mutane.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment