Sama Da Ƴan Bindiga 500 Ake Sa Ran Za Su Tuba Bayan Ganawa Da Shiekh Ahmad Gummi

Sama da ‘yan bindiga 500 ake sa ran za su tuba bayan ganawa da Shiekh Gumi

Rahotanni daga jihar Kaduna sun ce sama da ‘yan bindiga 500 ake sa ran za su tuba tare da ajiye makamansu, biyo bayan tattaunawa da fitaccen malamin addinin Musulunci Shiekh Ahmad Gumi a baya bayan nan.

Jaridar Desert Herald dake kan shafin internet a Najeriya ta ruwaito cewar ‘yan bindigar da ake sa ran za su tuba sune wadanda suka addabi babbar hanyar Zaria zuwa Giwa, da kuma karamar hukumar birnin Gwari.

Yayin taron wa’azin an baiwa jagororin ‘yan bindigar damar jawabi, inda bayanai suka nuna kusan dukkaninsu baki yazo daya wajen bayyana dalilan da suka tilasta musu daukar makamai, wadanda suka hada da cin zarafin da ake musu, kyara, kame su da jami’an tsaro ke yi ba bisa hakki ba tare da karbe musu kudade, sai kuma kisan gillar da wasu bata-garin jami’an tsaron ke musu.

A makwannin da suka gabata ne dai rahotanni suka ce Shiekh Ahmad Gumi yayi tattaki zuwa yankin Sabon Garin Yadi dake karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna, inda ya gabatar da wa’azi ga mazauna yankin, inda Fulani da dama ke zaune.Bayanai sun nuna cewar yunkurin Shaihin malamin na tunkarar warware matsalar ‘yan bindiga ta hanyar tattaunawa ya samu goyon bayan gwamnatin Najeriya da kuma hukumomin tsaron kasar, kamar yadda Jaridar Desert Herald ta ruwaito.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment