A gaggauce: Kwamishinan Tsaron Jihar Zamfara Da Harkokin Cikin Gida Ransa A Bace.

A gaggauce: Kwamishinan Tsaro Da Harkokin Cikin Gida Ransa A Bace.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Zamfara Abubakar Justice Dauran ya bayyana matsayin mummunan labarin da ‘yan jaridar Sahara suka wallafa a wata kafar yada labarai ta yanar gizo da ke zargin cewa Gwamnatin jihar Zamfara ta sayo Hilux ga wasu ‘yan ta’adda da suka tuba a matsayin labarin da ke cike da karya da kage.


Kwamishinan ya ce a bayyane yake cewa a duk fadin Najeriya, Zamfara ita ce kadai jihar da ta sayi motoci sama da 200 na aiki kuma ta ba da gudummawa ga jami’an tsaro don kawai a sami saukin gudanar da ayyukansu.

Ya ce akwai rashin daɗi idan ‘yan jarida sun yi zargin cewa gwamnatin data sayi wannan adadin motocin ga hukumomin tsaro zata iya ba da gudummawar motocin ga ‘yan ta’adda, Ya ce Ma’aikatar sa tare da hadin gwiwar ta Shari’a ba shakka za su dauki matakin shari’a akan labaran na yanar gizo. muddin suka kasa yin abunda ya kamata na bayarda hakuri.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment