Rangadin Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar Zamfara A Masarautar Gusau.

Kwamishinan Ƴan Sanda CP Abutu Yaro fcd, ya ziyar ci karamar hukumar Gusau domin kara samar da hanyoyin zaman lafiya mai dorewa a Jihar Zamfara Kwata.

Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau, Da CP Abutu Yaro.

A kokarinsa na tabbatar da haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki musamman Sarakunan Gargaji, Kwamishinan ƴan sanda CP Abutu Yaro fdc, da wakilin Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Zamfara, sun kai ziyara ta musamman a karamar hukumar mulkin Gusau domin samar da hanyoyin da za su kara samar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar Zamfara.

A lokacin Ziyarar, Kwamishinan ƴan sanda ya yi jawabi ga masarautar Gusau inda ya yi jinjina ga mai martaba Alh Ibrahim Bello Gusau, (Sarkin Gusau, Sarkin Gusau) na haɗin kai da masarautarsa take bayarwa ga hukumar ƴan sanda wajen ganin an samu zaman lafiya.Kwamishinan ya gabatar da wani babban kwamiti na musamman a Masarautar Gusau wanda zai dinga sauraron korafe-korafen bangaren fulani kai tsaye domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

A yayin ziyarar Kwamishinan ƴan sanda ya yi wata ganawa da Mayan jami’an yan sanda a babban ofishin Area Command dake Gusau take ƴan sandan na musamman ko yan sandan al’umma na Jihar Zamfara, ya ja hankalinsu tare da yi masu bayanin irin aikin da aka bukaci suyi. Kwamishinan ya yi wata ganawa da manya da kananan jami’an Rundunar ‘yan sanda ta Mopol ta jihar Zamfara

Da yake nashi Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Hon Abubara Dauran, wanda Permsec, Alhaji Musa Liman Shinkafi ya ke wakilta, ya yi kira ga al’umma da su daina tsangwamar yan uwa fulani wadan da suka rungumi zaman lafiya domin samun dai-daito a shirin Zaman lafiya da Gwamnatin jihar Zamfara ke gudanarwa.

A nashi martanin, Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau ya yi farin ciki sosai da ziyarar ta re da jinjina a garesa duba da irin tsare-tsaren da ya zo da Su wadan da suke nuni da cewa da gaske ya ke yi, Basaraken ya nuna goyon bayansa ga Kwamishinan ƴan sanda don cimma nasarar shirin samar da zaman lafiya a Jihar Zamfara. Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau ya yi kira ga majalisar masarautarsa na su yi sarda sakwanni zuwa ga al’ummar da suke jagoranta na irin tsare-tsaren da kwamishinan ya zo da su.

Taron dai ya samu halartar Kantoman Karamar Hukumar Mulkin Guusau Hon Sanusi Sarki da Uwayen kasa da hakimmai da masu ruwa da tsaki a masarautar Gusau.

📮 Abdulsamad Kabiru Musa
16-01-2021

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment