Adnan Oktar Mai Sinki-Sinkin Mata Har Guda Dubu (1000) An Yanke Masa Hukuncin Shekaru Dubu A Gidan Kaso
Adnan Oktar kenan wanda wata kotu a ƙasar Turkiya ta yanke masa hukuncin shekaru dubu a gidan kaso, laifukan da aka same shi da su, lalata da manya da kananan yara, karin laifukan da kotu ta samu Oktar mai shekaru 64 da aikatawa sun hada da, damfara da kuma yunkurin satar bayanan sirri na rundunar sojin Turkiya da kuma ‘yan siyasa, tare da mallakar yan mata har dubu, abinda ya sanya kotun yanke masa hukuncin daurin shekaru dubu 1 da 75.