Kwamishinan Ƴan Sanda Na Jihar Zamfara Ya Yi Rangadi A Shinkafi Da Zurmi

KWAMISHINAN YAN SANDA CP ABUTU YARO fcd, YA ZIYAR CI KANANAN HUKUMOMIN SHINKAFI DA ZURMI DOMIN KARA SAMAR DA HANYOYIN ZAMAN LAFIYA MAI DOREWA A JIHAR ZAMFARA.

A lokacin da Cp Abutu Yaro ya bude sabon ofishin Area Command a Shinkafi



A kokarinsa na tabbatar da hadin kai tsakanin masu ruwa da tsaki musamman Sarakunan Gargaji, Kwamishinan ‘yan sanda CP Abutu Yaro fdc, da wakilin Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, sun kai ziyara ta musamman a kananan hukumomin Shinkafi da Zurmi domin samar da hanyoyin da za su kara samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar Zamfara.

Cp Abutu Yaro a Masarautar Zurmi



A lokacin Ziyarar, Kwamishinan ‘yan sanda ya yi jawabi ga masarautun biyu inda ya yi jinjina ga sarakunan na hadin kai da suke bayarwa ga hukumar ‘yan sanda wajen ganin an samu zaman lafiya. A yayin ziyarar Kwamishinan yan sanda ya gana da sabbin ‘yan sandan Unguwa na kananan hukumomin biyu. Ya kuma yi wani taron tattaunawa da shugabannin Fulani, inda ya nemi goyon baya da hadin kansu don ciyar da shirin zaman lafiya da ake yi a Jihar Zamfara, inda ya gabatar da wani babban kwamiti na musamman wanda zai dinga sauraron korafe-korafen bangaren fulani kai tsaye domin samar da zaman lafiya mai dorewa.

Cp Abutu Yaro a Masarautar Shinkafi



Bayan kammala wannan Kwamishinan ‘Yan Sandan ya bude wani sabon katafaren ofishin Area Command a karamar hukumar Shinkafi.

Cp Abutu Yaro bayan ya bude sabon ofishin Area Command a Shinkafi



Da yake nashi jawabi wakilin Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Permsec, Alhaji Musa Liman Shinkafi, ya yi kira ga al’umma da su daina tsangwamar yan uwa fulani wadan da suka rungumi zaman lafiya domin samun dai-daito a shirin Zaman lafiya da Gwamnatin jihar Zamfara ke gudanarwa.

A nasu jawabin Kantomomin kananan hukumomin biyu sun nuna farin cikinsu tare da kara tabbatar ma kwamishina goyon bayansu da aiki tukuru domin samun nasara da zaman lafiya mai dorewa.

A nasu martanin, Sarakunan Shinkafi da Zurmi, sun yi alkawarin ba da goyon baya ga Gwamnatin Jiha da Kwamishinan ’Yan sanda don cimma nasarar shirin samar da zaman lafiya a Jihar Zamfara.

📮 Abdulsamad Kabiru Musa
11-01-2021

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment