An Kashe Ƴan Bindiga 50 Tare Da Kuɓutar Da Shanu 334 A Zamfara

Dakarun Sojojin Najeriya sun yi dauki ba daɗi da ƴan bindiga a Jihar Zamfara, inda suka kashe ƴan bindigar 50 a kauyen kurya cikin karamar hukumar Kaunara Namoda, sun samu nasarar kubutar da Shanun 334.

Hotunan shanun da aka kumutar

A wata sanarwa hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe ‘yan fashi 50 a ƙauyen Kuriya da ke Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara.

Sanarwar da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai, Manjo Janar John Enenche, ya fitar a yau Lahadi ta ce dakarunsu sun gwabza da miyagun ne tare da taimakon jiragen sama.

Ya ƙara da cewa soja huɗu sun ji raunuka yayin fafatawar, inda suka ƙwato dabbobi guda 334 da ‘yan bindigar suka sata.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment