Kwamishinan ‘Yan Sanda Na Jihar Zamfara Ya Yi Rangadi A Bakura DA Maru

KWAMISHINAN YAN SANDA CP ABUTU YARO fcd, YA ZIYAR CI KANANAN HUKUMOMIN MARU DA BAKURA, DOMIN KARA SAMAR DA HANYOYIN ZAMAN LAFIYA MAI DOREWA A JIHAR ZAMFARA.

Abutu Yaro Lokacin da yake zantawa da manema labarai

A kokarinsa na tabbatar da hadin kai tsakanin masu ruwa da tsaki musamman Sarakunan Gargaji, Kwamishinan ‘yan sanda CP Abutu Yaro fdc, da wakilin Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, su6n kai ziyara ta musamman a kananan hukumomin Maru da Bakura, domin samar da hanyoyin da za su kara samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar Zamfara.

Kwamishina tare da Mai Martaba Banagan Maru

A lokacin Ziyarar, Kwamishinan ‘yan sanda ya yi jawabi ga masarautun biyu inda ya yi jinjina ga sarakunan na hadin kai da suke bayarwa ga hukumar ‘yan sanda wajen ganin an samu zaman lafiya. A yayin ziyarar Kwamishinan yan sanda ya gana da sabbin ‘yan sandan Unguwa na kananan hukumomin biyu. Ya kuma yi wani taron tattaunawa da shugabannin Fulani, inda ya nemi goyon baya da hadin kansu don ciyar da shirin zaman lafiya da ake yi a Jihar Zamfara, inda ya gabatar da wani babban kwamiti na musamman wanda zai dinga sauraron korafe-korafen bangaren fulani kai tsaye domin samar da zaman lafiya mai dorewa.

Kwamishina a Masarautar Bakura

Da yake nashi jawabi wakilin Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Permsec, Alhaji Musa Liman Shinkafi ya yi kira ga al’umma da su daina tsangwamar yan uwa fulani wadan da suka rungumi zaman lafiya domin samun dai-daito a shirin Zaman lafiya da Gwamnatin jihar Zamfara ke gudanarwa.

A nasu martanin, Sarakunan Maru da Bukura, sun yi alkawarin ba da goyon baya ga Gwamnatin Jiha da Kwamishinan ’Yan sanda don cimma nasarar shirin samar da zaman lafiya a Jihar Zamfara.📮 Abdulsamad Kabiru Musa 09-01-2021

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment