An Karbo Mutane Takwas A Hannun ‘Yan Bindiga Sanadiyar Sulhu A Jihar Zamfara

A kokarin Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Hon Dr Bello Matawalle na ganin a samu Zaman lafita a Jihar ta hanyar sulhu an karbo mutane takwas 8 daga hannun ‘Yan bindiga, Wadan da aka karbo sun hada da Maza 4 Mata 4, an hannunta wadan nan mutane ga Maigirma Uban Kasar Karal dake Masarautar Gusau, Comrade Jamilu Aliyu, (Zanna Gusau, Ahijon Karal).

Da yake hannunta wadan nan mutane zuwa ga Uban Kasa a madadin Maigirma Gwamna Bello Matawall, Hon Abubakar Dauran (Justice) ( Kwamishina Tsaro Da Harkokin Cikin Gida) ya yi godiya ga ALLAH da wannan nasara da a kasamu a sanadiyar shirin zaman lafiya ta hanyar sulhu da gwamnatin jihar Zamfara take yi.

A nasa jawabi maigirma Uban Kasar Karal ya yi godiya ga ALLAH da samun wannan nasara na kubuta da wadan nan mutane nan take ya bada kyautar karramawa ta leshi babba da yadi ga wadan nan bayin ALLAH da aka karbo ta hanyar Sulhu.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment