Taƙaitaccen tarihin tshon shugaban Masar Hosni Mubarak

Cikakken sunansa shine Muhammad Honsi El Sayed Mubarak. An haifi shugaba Hosni Mubarek ne a ranar 4 ga watan Mayun 1928 a garin Kafr- ElMesselha dake ƙasar Masar. 

FB_IMG_1582661667428

ILMI 

Bayan ya kammala karatun sakandare ya shiga makarantar horas da hafsoshin jiragen sama ,inda ya samu digiri akan kimiyyar sojojin ƙasa a shekarar 1949.

A ranar 2 ga watan Fabrairu shekarar 1949 Hosni Mubarak ya bar makarantar sojin ƙasa inda ya koma makarantar da sojojin mayaƙan sama , inda ya kuma zama hafsan sojin sama mai muƙamin Pilot Officer a ranar 13 ga watan Maris ta shekarar 1950 , tare da kuma samun wani digirin a kimiyyar mayaƙan sama.

MUƘAMAI

A matsayinsa na hafsan sojin sama Mubarak ya riƙe muƙamai daban-daban. Kafin a shekarar 1959 inda ya tafi makarantar koyar da mayaƙan sama dake birnin Moscow dake ƙasar Rasha, da Bishkek da yanzu ke ƙasar Kirgistan domin koyon dabarun yaƙin sojojin sama.

Jiragen da Mubarak ya kware wajen sarrafasu a wancan loƙacin sun haɗa da Tupolev Tu-16 .

Bayan komawarsa gida a shekarar 1964 ya zama kwamandan makarantar horas da mayaƙan sama na ƙasar Masar a sansanonin daban-daban dake faɗin ƙasar.

A shekarar 1967 Hosni Mubarak ya zama babban kwamandan dakarun sojojin sama na ƙasar Masar , kafin kuma daga bisani ya zama babban hafsan haɗin gwiwar sojin ƙasar baki ɗaya kuma mataimakin ministan tsaro. An yiwa Hosni Mubarek ƙarin girma zuwa Air Marshal bisa gudunmawar daya taka a loƙacin yaƙin Yom Kippur.

SHUGABANCI

Bayan kisan gillar da masu kishin addini suka yiwa shugaban Masar na wancan loƙacin Anwar Sadat a shekarar 1981 , Hosni Mubarak ya zama shugaban ƙasar Masar kuma jagoran jam’iyyar National Democratic Party.

Hosni Mubarak shine shugaban ƙasar Masar mafi daɗewa a gadon mulki wanda ya kwashe shekaru 30 , bayan Muhammad Ali Pasha wanda ya jagoranci ƙasar shekaru 43 daga shekarar 1805 zuwaɓ1848.

Hosni Mubarak yabar kan karagar mulkin ƙasar a shekarar 2011 bayan kwanaki 18 da zanga-zangar ƙin gwamnatinsa

IYALAI

Hosni Mubarek yana da mace ɗaya mai suna Suzanne Mubarak da ƴaƴa biyu maza : Alaa da Gamal Mubarak.

RASUWA

Hosni Mubarak ya rasu a yau 25/2/2020 yana da shekaru 91 a duniya

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment