Gwamanan Jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya yi kira ga gwamnatin tarayya a karkashim shugaban kasa Muhammad Buhari da ta kirkiro dokokin da za su halasta ta’ammali da tabar wiwi a Najeriya.
Gwamna Rotimi ya bayyana haka ne yayin ziyara da ya kai fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a ranar Talata 4 ga watan Feburairu 2020, inda ya yi ganawar sirri da shugaban kasa Buhari a ofiahinsa, inda ya ce “Jaharsa za ta zuba hannun jari don had a magungunan kwayoyi daga tabar wiwin.