Marayu 658 za su samu tallafin ₦Miliyan 164 a Zamfara

Mai Daraja Gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ya kaddamar da shirin baiwa marayu dari shida da hamsin da Takwas (658).


Tallafin Wanda wata kungiya Mai mazauni a kasar saudiya Mai suna International Relief Organization. Mai ofishi a jahar Kaduna a nan Nigeria.

Wanda tallafi dai an yi Rigistar wadanda na amfana da shi tun lokacin mulkin Tsohon Gwamnan jahar Mamuda Aliyu Shinkafi, Wanda aka zakulo wadanda su ka amfana daga kananan hukumomin jahar 9 kuma kowane daga cikin marayun ya amfana da naira dubu Dari biyu da hamsin (250)

Da ya ke jawabi jakadan wannan kungiyar a Najeriya Sheikh Dr. Abdullahi Bn Salim, ya nuna farin cikinsa da akan irin kyakkyawan tarba da ya samu daga gwamnatin jahar tare da yabawa Gwamna akan yadda ya sadaukar da Rabin albashinsa ga marayun jahar Zamfara, Wanda ya haifar da kyautata rayuwar marayun jahar. Haka Zalika ya bayyana cewa wannan rukunin A ne na wannan aikin. Sauran rukunnan na tafe. Kuma wadannan makuddan kudade masu hannu da shuni ne, daga kasar saudiya ke bayar da tallafinsu, ga marayu a kasashe masu tasowa.

Da yake jawabi Mai Daraja Gwamnan jahar Zamfara, ya bayyana matukar godiyarsa ga wannan kungiyar, tare alkawarin ba su goyon baya dari-bisa-Dari dari, ta hanyar bayar da gudunmawar gwamnatin jahar Zamfara, haka Zalika ya Kira ga kungiyar, ta shigo jahar Zamfara wajen tallafawa masu Dan karamin karfi akan matsalar rashe-rashen rayukka da dukiyoyin da ya Faru a jahar Zamfara. Ta hanyar Gina masallatai, makarantanni tare da gina garuruwan da su ka zama turbaya.

Taron dai ya samu halartar Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau. Alh. Ibrahim Bello Gusau, Kakakin majalissar dokokin jahar Zamfara Rt Hon. Nasiru Mu’azu Magarya, Sakataren gwamnatin jahar Zamfara, Hon. Bala Bello Maru, Shugaban Ma’aikatan jahar Zamfara Alh. Kabiru Balarabe, Kwamishinoni da Manyan masu ba Gwamna Shawara da su marayun da kuma Sauran muhimman Jama’a.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment