Zhou Pingjin Jekadan kasar China a Najeriya, ya ce ” Ofishin Jekadancin kasar ta dakatar da ba ‘yan Najeriya biza.
“Ya ce hakan yana daga cikin kokarin da ake na magance cutar coronavirus da ya bullo a kasar Asiya”.
Sama da mutane dari ukku ne suka mutu sanadin mummunar annobar a China, yayin da kungiyar lafiya ta Duniya ta kaddamar da shi a matsayin matsalar Duniya kasa da mako guda bayan gwamnatin kasar Amuruka ta sanya haramcin bayar da biza ga ‘yan Najeriya da wasu kasashen Afrika.