Gina Filin Jirgi Da Sabon Gidan Gwamnati A Zamfara Babu Fashi – Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara, Hon. Bello Muhammad Matawalen Maradun, ya jaddada cewa, gina sabon gidan gwamnati da filin jirgin sama a Zamfara ba gudu babu ja da baya ko nawa za a kashe, domin, a cewarsa, alheri ne ga al’umma.

Gwamna Matawallen Maradun ya bayyana haka ne a gidan gwamnatin jihar lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Gwamnan ya kara da cewa, Jihar Zamfara na da bukatar sabon gidan gwamnati da isassun ofisoshi da masaukin baki da masaukin Shugaban Kasa, domin rashin tanadin wadannan abubuwa na jawo wa jihar nakasu.

Ya ce, “abin kunya ne idan mun yi manyan baki mu kai su otel. Don haka ko nawa za mu kashe wajen samar da gidan gwamnati, za mu kashe. Duk masu korafe-korafe a kafafen sadarwa, su cigaba; kada su fasa, mu ma ba za mu fasa ba.” Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa, aiki zai yi da kudin al’umma, don amfanar al’umma, ba zai bari wasu su sace kudin jama’a ba.

Kuma ya kalubalanci masu cewa, za a kashe Naira biliyan shida wajen gina gidan gwamnati, don a gwamnatin baya ta gina titin By Pass ta Talata Mafara kilomita tara a kan Naira biyan 11, duk da ba shi ne matsalar al’ummar karamar hukumar ba, “amma mutane ba su yi tsegumi ba, sai mu da za mu gina gidan gwamnati,” in ji shi. Da ya koma kan batun gina filin Jirgin Sama, Gwamnan Matawallen Maradun ya bayyana cewa, “duk masu son zuwa Zamfara, don zuba hannun jari su na tambayarmu cewa, daga Abuja zuwa Zamfara awa nawa ne a jirgin sama? Sai mu yi shiru.

Wannan ya tabbatar da cewa, lallai cigaban da mu ke son kawowa ba zai yiwu ba sai da filin jirgin sama. “Don haka ne ya zamo dole mu samar da shi a wannan jihar tamu, kuma a nan Arewa kusan mu ne kadai wadanda ba su da filing jirgin sama.”

A kalaman bakinsa, “cece-kuce da rubuce rubuce ba zai hana mu yin ayyukan cigaban al’ummar jihar Zamfara ba.”

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment