A labarin duminsa ya bayyana cewa cinkoson jama’a sosai da kuma surutunsu ya sanya kotun Kolin Nijeriya ta dage zaman da ta fara yau na yanke hukuncin shari’ar zaben wasu gwamnonin Nijeriya da ta fara yi a yau.
Alkalin-Alkalan Nijeriya Mai Shari’a Ibrahim Tanko dake jagorantar masu shari’a 7 ne ya bayyana dage zaman a zauren kotun Kolin.
Ya kuma bayyana wa masu kara da wadanda ake kara kada kowannensu ya wuce lauyoyi biyar, da kuma wakilan jamiyya kadai a zama na gaba
Za a iya tuna cewa da a yau ne kotun ke yanke hukuncin shari’ar zaben gwamnan jihar Kano, da Sokoto, da Plateau da Imo da Bauchi da da Benue .
Za a cigaba da zaman zuwa gobe talata