Wani Limami ya auri namiji a bisa rashin sani

An dakatar da wani limami a Uganda, wanda ya auri namijin da a tunaninsa mace ce, kamar yadda jaridar Daily Monitor ta rawaito.

Sheikh Mohammed Mutumba ya kadu da ya gano cewa matarsa Swabullah Nabukeera namiji ne mai suna Richard Tumushabe tsawon mako biyu da auren, a cewar jaridar.

Lamarin dai ya faru ne bayan da ‘yan sanda suka kame Tumushabe bisa zarginsa da satar akwatin talabijin da wasu kayan sawa daga makwabcin gidan da yake aure.

A cewar Misis Mugera: “Kamar yadda ‘yan sanda suka saba, ‘yar sanda ce ta caje wadda ake zargin kafin kai ta dakin tsare wadanda ake zargi da aikata laifi.

Sai dai ga mamakin ‘yar sandar, wadda ake zargin badda kama ta yi ta yi shigar mata.”

Sheikh Mutumba – limami a wani masallaci da ke kauyen Kyampisi, mai nisan kilomita 100, arewa maso yammacin birnin Kampala – bai taba saduwa da amaryar tasa ba saboda ta ce tana al’ada, in ji rahoton da jaridar ta wallafa.

An rawaito Misis Mugera da cewa “Mun riga mun tuhume shi da shigar mata da sata da kuma zamba.”

Jaridar Daily Monitor ta ce Sheikh Abdul Noor Kakande, alkalin kotun Musulunci ya ce lamarin abin takaici ne kuma shi ma limamin, ana bincike a kansa.

Jaridar ta kuma rawaito Sheikh Isa Busuulwa, babban limanin masallacin da Sheikh Mutumba ke wa’azi na cewa an dakatar da shi domin kare martabar addinin Musulunci.

Daily Monitor ta bayyana cewa rabon Sheikh Mutumba da gida tun kwanaki hudu da suka gabata.

Wata majiya da ba a bayyana sunanta ba ta ce “ya dimauta da lamarin kuma yana bukatar a ba shi shawara”.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment