Rundunar yan sandan Nijeriya reshen jihar Sokoto ta bayyana cewa a yanzun haka ta barbaza jami’aat a kalla guda 1000 a cikin gari da kewayen jihar, bisa tabbatar da kyakkyawan tsaro bayan Kotun Koli ta yi hukuncin karshe kan wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka yi a 2019.
Dan takarar jam’iyyar APC Ahmed Aliyu ne ya shigar da zababben gwamnan jihar Tambuwal na jamiyyar PDP a kotun yana kalubalntar nasarar da ya samu.
A gobe Litinin ne dai ake sa ran babbar kotun Kolin Nijeriya za ta yi hukunci na karshe a kan halastatcan gwamnan na jihar Sokoton