Kamar tatsuniya:Wani Pastor ya kashe shedan mutus har la ila.

Pastor Mboro dake kasar South Africa ya bayyana cewa ya ziyarci Jahannama har ya samu nasarar farfasawa Shedan baki, wai yana shiga Jahannama sai ya hango wasu manya manyan kasar South Africa da sukayi mulki kuma sukayi rayuwa mai tsada anan duniya dukkansu a cikin Jahannama suna karbar gashi.

Labarin da jaridar Zambianobserver ta ruwaito.


Wai da shedan ya hangoshi ya shigo Jahannama ssi ya turo wasu dakaru da niyyar su fitar dashi Pastor daga cikin wutar, amma nan da nan sai ya alkafira ya dinga suburbudarsu har sai daya kashesu gaba daya, sannan ya karasa inda shedan yake, nan ma dai ya dinga makashi da kasa har sai daya kasheshi….

Pastor Mboro yace yanzu kowq dake kasar South Africa ya kwantar da hankalinsa, domin dai ya kashe Shedan, yanzu babu sauran jin tsoron aikata laifi, tunda shedan mai sanyawa a aikata laifi ya mutu…..

Yanzu dai an hango mabiya Pastor cikin murna da annushuwa tun bayan daya sanar dasu cewa ya kashe shedan….

Sai a shiga wannan link da jaridar Zambianobserver ta ruwaitao

Pastor Mboro allegedly visits hell, battled and killed satan

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment