A Najeriya za’a fara samun wutar lantarki ta tsawon awa 18 kullum a kwanan nan

Ministan hasken lantarki, Injiniya Sale Mamman ya ce, akwai yiwuwar ‘yan Nijeriya za su fara samun hasken lantarki na tsawon awanni 18 a kullum da zaran hukumar samar da hasken lantarkin da rarraba shi ta samu megawatt 7,000 na hasken lantarkin.

Ministan ya bayar da tabbacin ana samun ci gaba matuka a sashen na samar da hasken lantarki. “Ta fuskacin gwamnati, muna kokari matuka wajen inganta lamarin, don haka nake cewa ya zuwa karshen wannan shekarar za mu sami akalla megawatt 7,000. “Daga kuwa lokacin da muka sami hakan, akwai yiwuwar mu rika samun hasken lantarkin na tsawon awanni 18 a kullum, domin a lokacin muna da megawatt 11,000, don haka kowa zai samu isasshen hasken lantarki kuma wadatacce,” in ji Injiniya Mamman Sale, da yake kara bayar da tabbacin hakan.

A kan shirin yin karin kudin hasken lantarkin, Ministan cewa ya yi kamfanonin rarraba hasken lantarkin da kuma hukumar kula da hasken lantarkin ta kasa sun kulla wata yarjejeniya a lokacin siyar da kamfanin. “Yanzun wannan maganar ba a hannun gwamnati ne take ba, saboda kashi 60 yana hannun ‘yan kasuwa ne, sai dai muna sa ido ne kawai. Mu dai namu shi ne mu tabbatar da komai yana tafiya daidai kamar na sauran kasashe.

Muna kuma gayyatar masu zuba jari da su zo, in kuma ba mu yi hakan ba (karin kudin lantarkin), sam ba za su zo ba, amma dai ina da tabbacin ba za mu yi abin da ya wuce ka’ida ba. Ministan ya ce, batun ingantawa da fadada sashen zai baiwa kamfanonin rarraba hasken lantarkin damar dogaro da kansu. “A shekarar 2018, gwamnatin tarayya ta bayar da naira bilyan 700 domin cike gibin da ke a tsakanin kamfanin samar da hasken lantarkin da kuma kamfanonin rarraba hasken lantarkin, domin ya zama tilas ga kamfanin samar da hasken lantarkin ya rika biyan kudin Gas.

Hakan kuma ba abu ne da za a iya ci gaba da shi ba, a shekarar da ta wucen mun karbi naira bilyan 600 domin cike gibin,” in ji Ministan. Mamman ya ce aikin dubawa da tantancewa na tashar samar da hasken lantarki ta Mambila, mai karfin megawatt 3050 za a kammala shi ne a nan da watanni biyu, inda kuma biyan kudaden fansa ga mutanan da abin ya shafa zai biyo baya da zaran an kammala din.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment