Gwamnatin hadin kan kasa a Libiya ta cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da dakarun sojin Janar Khalifa Haftar da ke kan bakansu na kwace iko da babbab birnin kasar.
Bangarorin biyu da suka dau lokaci suna gwabza fada kan iko da Tripoli sun cimma matsaya na dakatar da fada bayan da wata yarjejeniya da kasashen Turkiyya da Rasha suka shiga tsakani.
Sai dai Janar Haftar ya ja kunnen bangaren gwamnatin da ke samun goyon abyan Majalisar Dinkin Duniya za su su fuskanci martani mai tsanani idan suka yi karambanin sake tada rikici.