‘Yan Ofereshin Hadarin Daji, sun kashe sama da yan ta’adda 100, a dajin Zamfara da Katsina

Akalla an kashe yan ta’adda su 100, masu fashi da makami da kuma garku da mutane a yankin jihar Zamfara da kuma makwabciyarta jihar, Katsina.


Rundunar hada ka ta Ofereshin Hadarin Daji ta bayyana wannan nasarar da ta samu daga watan Disamban 2019 da ya gabata zuwa Janairun 2020 din da muke ciki.

Mukaddashin mai magana da yawun rundunar hada kan Ayobami Oni-Orisan, shi ye ya bayyana haka a lokacin da suka kira taron manema labarai yau Asabar a birnin Gusau.

Ya kara da cewa daga cikin jami’an tsaron dake cikin Ofereshin Hadarin Dajin akwai, sojojin kasa, da sojojin sama, da na ruwa, da kuma jami’an yan sandan Nijeriya da DSS da sauran wasu jami’an tsaron da aka hadu aka sami wannan gagarumar nasarar.

Mai magana da yawun rundunar hada-kan, ya kuma ce sun yi nasarar ceto mutum goma da aka yi garkuwa da su, sannan sun kwato sama da shanu 600, da tumakai 300, da barayin suka sace, gami da kwato muggan makamai a hannun yan bindigar.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment