Mata Baƙake Sun Fi Kowa Kyau A Duniya- Ƙwararriya

Princess Ronke Ademiluyi, wadda ta samar kuma shugabar Africa Fashion Week London/Nigeria ta bayyana mata baƙaƙe a matsayin waɗanda suka fi kowa kyau a duniya.


Misis Ademiluyi ta faɗa wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, haka a wani taron kwana biyu na 2019 Africa Fashion Week London Nigeria da aka yi a Legas.

A ta bakinta, yadda mata baƙaƙe suka lashe kyaututtuka biyar mafiya girma a Gasar Sarauniyar Kyau da aka kammala kwanan nan ya tabbatar da haka.

Ta ce alfaharin mata baƙaƙe, wanda ya fara tun a 2001, da ‘yar Najeriya, Agbani Darego, ya fito kwanan nan lokacin da Miss Jamaica, Toni-Ann Singh ta lashe Gasar Sarauniyar Kyau ta Miss World ta 2019 a Landan.

“Baƙi shi ne kyau na zahiri, ba kawai a fuska ba, amma har a ido, kuma haka ne yasa mashahuran masu kayan ƙawa suka yi fice ta hanyar amfani da baƙaƙe a matsayin samfur don siyar da kayayyakinsu.

“Mata baƙaƙe su suka fi kowa kyau a duniya da za su iya ciyar da kwalliyar Afirka zuwa mataki na gaba”, ta ƙara da haka.

Da take jawabi a game da Africa Fashion Week Nigeria, Misis Ademiluyi ta ce kayan ƙawa na Afirka za su iya yin gasa da sauran kayan ƙawa na duniya.

“Kayanmu na ƙawa suna da ban mamaki. Masu haɗa kawa na Afrika sun taso. Maganar gaskiya, za su iya yin daidai da duk wani tufafi na ƙasashen Turai.

“Kayanmu babu irin su kuma za su iya siyuwa duk duniya. Ko lokacin da muka yi bukukuwan baje kolin ƙawa a Landan, kayan ƙawarmu da na kwalliya sun samu karɓuwa sosai, kuma an neme su”, in ji ta.

Misis Ademiluyi, wadda kuma ita ce Jakadiyar Kula da Al’adu ta Qeen Moremi Ajasoro, ta faɗa wa NAN cewa babban taron nuna kayan ƙawar zai nuna wasu matan shugabannin Najeriya na amfani da Africa Fashion Week Nigeria don haɓaka kyawawan halaye.

“Matan gwamnonin Ekiti da Kwara za su shirya tarukan baje kolin kayan ƙawa, kuma gwamnoni za su halarta.

“Babban Uban Ƙungiyarmu kuma Maimartaba, Ooni na Ife zai halarci taron shi da tawagarsa”, in ji ta.

NAN ya ruwaito cewa 2019 African Fashion Week London/ Nigeria shi ne karo na shida tunda aka fara shi

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment