Dan majalisa a Zamfara ya tallafawa mata 50 da kayan sana’a

Dan majalisa mai wakiltar Gusau da Tsafe a majalisar dokokin tarayyar Najeriya, Hon Kabiru Amadu Mai Place, ya tallafawa mata 50 da kayan Sana’a wasu da kudin jari domin dogaro da kansu.


Kaman yanda yasha Alkawurrantawa a lokacin yakim neman zabensa zaiyi iya kokarinsa na ganin ya kawar da matsalar Rashin Sana’ar yi ga iyayenmu mata yauma dan Majalisar mai wakiltar Gusau da Tsafe ya kaddamar da bayar da tallafi ga wasu mata guda hamsin daya dauki nauyin koya masu sana’o’in hannu a wata cibiyar Koyar da mata sana’o’in hannu dake unguwar premier Road karkashin Jagoranci Hajiya Zainab Janyau.


A wajen Bayarda Tallafin Dan Majalisar Ya Jaddada cewa baiga dalilin da zaisa yaje Majalisa yayi tunanin cewa zai tara abun duniya ba Alhali ga Al-ummar sa na cikin matsanancin halin bukatar taimako, ya kara da cewa a kullum al-ummar sa sune ke gabansa kuma zaiyi kokarin ganin a cikin shekarunsa hudu na zamansa Majalisa ya cika alkawurran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe, haka zalika ya kara da cewa nan gaba kadan jerin wasu mata dari biyar (500) zasu fita daga halin rashin sana’aryi kasancewa dukkan shirye shirye sun kankama na ganin cewa an tallafawa iyayenmu mata domin ganin sun fita daga halin rashin sana’ar yi dake addabar su.


A wajen wannan bukin kayan da aka bayar sun hada da

☆ Teloli Kwara Goma Sha Biyar (15)

☆ Injunan Tsaka Goma Sha Biyar (15)

☆ Kayan yin Hypo da Izol ga Macce Asirin da Kudi Naira Dubu Ashirin ga kowaccensu (20,000)

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment