Gwamna Matawalle ya ja kunnen tsohon Gwamnan Zamfara AA yari

Da marecen jiya alhamis ne 21-11-2019, daya daga cikin jiga-jigan ‘yan ta’addar da su ka Hana Zamfara Zama lafiya, ya rungumi shirin sulhu Wanda gwamnatin jahar ke yi. Tare da Mika Manyan bindigoginsa ga gwamnatin jahar.


Da ya ke jawabi mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun, ya nuna jin dadinsa ga wannan Tsohon Dan ta’adda da ya Mika mukamansa tare da alkawarin taimakawa shirin zaman lafiya na jahar.

Haka zalika gwamnan ya yi kira da babbar murya da Jan kunnen zuwa ga Tsohon gwamnan jahar Zamfara da ya shiga taitayinsa. Domin gwamnatinsa ba za ta zura ido ba. Ga irin kutun guilar da su ke yi Don ganin Zamfara ba ta zauna lafiya ba.

Inda ya bayyana Cewa Karo uku kenan Tsohon gwamnan na shigowa Zamfara, amma duk ya zo Sai an samu Matsala Kuma ranar da aka samu Matsala ranar zai gudu ya tafi, zai zo ya yi taro da mutane a Mafara daga nan ya yi meeting da barayi su tafi su addabi Al’umma.

Dan haka gwamnan ya yi kira ga Tsohon gwamnan da kada ya yarda ya kara irin hakan in Kuma haka ta kara faruwa to gwamnatinsa za ta dauki kwakkwaran mataki akansa.

Taron Mika mukaman da mubayi’ar wannan dan bindigar dai ya samu halartar Kwamishin ‘yan Sanda na jahar Zamfara Usman na Gwaggo, Babban mai baiwa gwamna shawara Akan sha’anin tsaro. Hon. Abubakar Dauran Justice da Sauran Manyan makaraban gwamnatin Zamfara.

Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Executive Governor Of Zamfara State

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

2 thoughts on “Gwamna Matawalle ya ja kunnen tsohon Gwamnan Zamfara AA yari

Leave a comment