Za a koma zaman majalisar Jahar Zamfara a makarantar firamare

Majalisar Jahar Zamfara za ta koma wata makarantar firamare inda za ta dinga aiwatar da zaman majalisar da sauran harkokinta.

fb_img_1582279616185-18794786597287450393.jpg

Hakan ya biyo bayan fara gyaran zauren majalisar da za a yi. 

Gwamna Dr Bello Muhammad Matawalle ya bada kwangilar gyaran ginin zauren majalisar.

Wannan ya biyo bukatar da Faruku Dosara, ahugaban masu rinjaye na majalisar ya mika.

“Ina so in jawo hankalin abokan aikina na bukatar mu koma wani waje daban sakamakon sakamakon gyaran zauren majalisa da ake yi, ” in ji Dosara.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment