Gwamnatin Zamfara za ta samar da Asibitoci 147

Gwamnan jihar Zamfara Hon Dr. Bello Mohammed MON (Matawallen Maradun) ya bayyana cewa, gwamnatin sa ta kammala shirin samar da asibitoci 147 a fadin Jihar don inganta harkokin kiwon lafiya musamman ga mazauna yankunan karkarar a jihar.

Bayanin haka na kunshe ne a takardar manema Labarai da mai ba Gwamnan shawara na musamman a kan harkokin watsa labarai Alhaji Yusuf Idris ya sanya wa hannu aka kuma raba wa ‘yan jaridar a Gusau. Sanarwar ta kuma cigaba da bayyana cewa, Gwamnan ya yi bayanin haka ne yayin da yake karbar Kasiloli 5 daga karamar Hukumar Gusau da suka sauya sheka daga jamiyyar APC zuwa jamiyyar PDP a gidansa dake garin Gusau. Gwamna Matawalle ya ce, a halin yanzu an kammala dukkan shirye shirye na fara ginin asibitocin guda 147 don bunkasa shirin gwamnati na samar da kiwon lafiya a yankunan karkara.

Ya kuma kara da cewa, asibitocin za su sami katfin karba tare da kwantar da marasa lafiya masu fama da kananan cututtuka, hakan kuma zai rage wahalar da suke fuskanta na neman magani a manyan asibitocin birane.

Matawalle ya kuma bayyana cewa Gwamnatinsa a shirye take na ganin ta samar wa da alumma jihar cibiyoyin kiwon lafiya masu inganci a dukkan mataki. Gwamna ya kuma bayyana cewa Gwamnatinsa sa za ta samar da cigaba a dukkan mazabu 147 dake fadin jihar. Daga nan ya bukaci kansilolin da su cigaba da ba gwamnati shawarwari masu mahimmanci don bunkasa jihar.

Ya kuma nuna jin dadinsa a bisa shawarar kansilolin na shigowa jamiyyarsa na PDP daga jamiyyar adawa ta APC , ya kuma yi musilu alkawarin tafiya tare da su ba tare da nuna banbanci ba. Kansilolin da suka sauya shekan sun hada da Hon. Ibrahim Kogo na mazabar Wonaka, Hon.Yahaya Aliyu na Madawaki, Hon. Shehu Isah Wanda aka fi sani da (Shehu Leda) na mazabar Sabon Gari, Hon. Abdulhamid Sani na mazabar Ruwan Bore da kuma Hon.Shamsu Umar na mazabar Rijiya Ward.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment