Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da kwangilar gina gidaje 10,000 a jihar Borno a cikin yunkurin da gwamnatin tarayya ke yi na farfado da jihar bayan barnar da ta’addancin Boko Haram ya yi.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umaru Zulum ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a 10 ga watan Janairu a shafinsa na Twitter.
Shugaban kasar ya yi wannan umurnin ne bayan Zulum ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira a ranar Alhamis, 9 ga watan Janairu inda ya kwana a can yana taimakawa wurin rabon kayan tallafi ga kimanin iyalai 1675.
Gwamnan ya kuma yi rabon barguna da daduma ga ‘yan yi wa kasa hidima a jihar don taimaka musu magance sanyi a wannan yanayin na hunturu.
Ya kuma tabbatarwa ‘yan gudun hijirar cewa yana nan kan bakansa na kokarin ganin an mayar da su garuruwansu idan an gama gine-gine.
Kazalika, Zulum ya yi wa ‘yan gudun hijiran alkawarin cewa gwamnatin tarayya na iya kokarin ta don ganin ta kawoi karshen ta’addanci a jihar da sauran sassan kasar.
Gwamnan jihar na Borno ya kuma yabawa rundunar sojojin Najeriya kan matakin da ta dauka na gudanar da bincike kan zargin karbar kudade a hannun matafiya da ake ce sojoji na yi.
Majiyarmu ga Legit. ng ta gano cewa Zulum ya yi wannan jawabin ne a daren Litinin 6 ga watan Janairu bayan mai kula da fanin yada labarai na soji, Aminu Iliyasu ya fitar da sanarwa.