Gov, Aminu Tambuwal Sokoto ya aminta da fara biyan ₦30k mafi karancin albashi

Gwamna Tambuwal Yace watanni baya ya dau alkawalin biyan Sabon mafi karancin albashi na Naira dubu 30 kuma gashi lokacin yayi na cika alkawalin. Don haka zaa soma biyan a wannna Watan na January.


Gwamna Tambuwal yace zaa biya duk maaikacin gaskiya ko wata nawa zai dauka idan an gani shi zaa biya shi a binciken da ake.

Gwamna Rt.Hon.Aminu Waziri Tambuwal ya gode ma Shugaba da Membobin Kwamitin da aka kafa don gyara tsarin albashi da aiwatar da sabon karin albashin akan hubbasar su.

Gwamna Rt.Hon.Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya karbi rahoton Kwamitin Gyara Albashi da aiwatar da Sabon Albashi na Naira dubu 30 ga Maaikatan jihar Sokoto.

Taron Wanda Kakakin Majalisar Dokoki na jihar Sokoto Rt.Hon.Aminu Muhammad Achida da Sakataren Gwamnatin jihar Sokoto Malam. Saidu Umar da Membobin Majalisar Zartarwa ta jihar Sokoto da masu baiwa Gwamna Shawara. Wanda aka gudanar a dakin taro na Gwamnatin jihar Sokoto.

A wajen mika rahoton Shugabanin Hukumomi da kungiyoyin Maaikata dake da Ruwa da Tsaki da hakkin albashi suka saka hannu ga rahoton Kwamitin don nuna amincewar su ga duk matsayar da aka cimma akai tsakanin Gwamantin jihar Sokoto da Kwamitin gyaran albashi da Kungiyoyin kwadago da na yan kasuwa akan Sabon albashin.

A jawabin sa Shugaban Kwamitin gyaran albashi na jihar Sokoto Alh. Namadina Abdulrahman yace a satin 3 da kafa Kwamitin sun dauki lokaci suna kokarin cimma lokacin da aka basu, don kawo magana daya akan Sabon albashi a Sokoto.

Yace Duk bayani da ya kamata kwamitin ya samu daga Bangarorin Hukumomi Gwamnatin da na Kungiyoyin Maaikata.

Yace Kwamitin ya amince da Naira Miliyan 320 da ake bukata kari don samun biyan Sabon tsarin Albashi na Naira dubu 30 a Sokoto ba kamar yadda Kungiyar kwadago ta bukata na Naira Miliyan 340 ba.

Yace dole a Nemo hanyoyin samun Kudaden shiga Wanda Majalisar Dokoki ta jihar Sokoto ke kan yin Dokoki akai.

Kwamitin ya bada shawarar a kafa Kwamitin tabbatar da duk abubuwan da Kwamitin su ya gano don samun nasarar ga Sabon albashi da kuma samun Karin Kudaden shiga ga jihar Sokoto.

Yace Kwamitin ya bada da shawara a Soma Biyan Sabon Albashi daga Watan nan na January.

Taron ya samu halartar Tsohon Mataimakin Gwamnna jihar Sokoto Alh. Ahmed Muhammad Gusau,Tsohon Minister Alh. Eng. Bello Sulaiman Shugaban Jamiyar PDP na jiha Alh Ibrahim Milgoma da Sauran Yan Kwamitin Gyaran Albashi da aiwatar dashi, Shugabanin Kungiyar Kwadago na jihar Sokoto.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment