Wata sabuwa: Za’a tsige Shugaba Buhari kafin karshen 2020

Babban faston cocin Chirst Foundation Miracle International Chapel, dake jihar Legas, Prophet Josiah Onuoha Chukwuma ya bayyana shugaban kasa Muhammad Buhari zai bar ofis kafin karshen shekarar 2020.

A cewar shi, shugaban kasar zai iya tsallake wannan matsala ne idan har ya iya jure matsalar da za ta taso a karshen watan Nuwambar 2020.

Chukuma, wanda yayi magana da Chinedu Adonu a Enugu, ya kuma yi kira Orji Uzor Kalu da kuma shugaban kamfanin jirgin sama na Air Peace, Chief Allen Onyema, da suyi gaggawa su ceto rayuwarsu da kuma kasuwancinsu daga fadawa wani hali.

Ga abinda ya ce:

“Na ga babbar matsala da tashin hankali, Buhari ya bi a hankali. Idan mai girma shugaban kasa ya samu ya tsallake tashin hankalin dake tunkaro shi, kamar yadda Allah ya nuna mini, daga nan zuwa karshen watan Nuwamba, to akwai yiwuwar zai iya ceto mutanen shi. Amma a halin yanzu abinda nake gani shine, Buhari zai bar ofis, ko ta hanyar tsige shi ko kuma ta hanyar rashin lafiya. Wannan shine iya abinda zan iya cewa.”

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment