Dalilin gina sabon gidan Gwamnati a Zamfara

Korafe-korafe sun cika dandalin sada zumunta akan kudurin gwamnatin jihar Zamfara na gina katafaren gidan gwamnati wanda a hakikanin gaskiya akasarin masu korafin basu fahimci yanayin da ake ciki ba game da harkokin gudanar da mulki da bukatun da suka wajaba wajen gudanarwar


Da yawa wasu ba su san cewa tun lokacin da aka samu jihar Zamfara a 1996 babu wani takamammen gidan gwamnati da aka gina, hasali ma inda ake yanzu mazaunin sakatariyar karamar hukumar mulki ta Gusau ne aka yi wa kwaskwarima don zama gidan gwamnati na waccan-gadi kafin a gina ta dindindin.

Gina sabon gidan gwamnati a yanzu zai samar da wadataccen wuri da zai sanadiyar samun rarar makudan kudi da ake kashewa wajen biyan kudin hayar ofisoshi da gwamnati ke biya a cikin garin Gusau. Dalilin karancin wuraren gudanar da sha’anin mulki ne yayi sanadin gadar bashin Naira Miliyan Dari Takwas (₦800,000,000) na hayar ofis ofis daga gwamnatin da ta gabata. Idan haka zai dore ba a san inda adadin kudin za su kai ba.

Ya kamata a lura da cewa, gwamnatin da ta gabata ta yi kudurin gina sabon gidan gwamnati har ma ta kebe fili. Zuwan gwamnatin Dr Bello Matawalle aka fahimci bukatar gina gidan saboda bai kamata ace a cigaba tafiya haka tsawo da shekara Ashirin da Uku babu gidan gwamnati da ya dace da zamani. Dalilin haka Gwamna Bello Matawalle ya samar da gurbin yin aikin a cikin kasafin kudi na shekarar 2020.

Sabon gidan gwamnati da ake shirin yi zai zamo wani katafaren sansani da ke kunshe da ofis ofis, dakunan taro, masaukai, gidaje da sauraran su wadanda za su bada hurumin taron kowane bako daga ko’ina cikin karramawa.

Sanin kowa ne Gwamna Bello Matawalle ba don kan sa zai gina gidan ba don ya wadatu daga haka sai dai ita gwamnati tana bukatar ganin ta shiga tsara kuma ta kai karshen yawan daukar nauyin biyan hayan ofis-ofis.

Ibrahim Bello Zauma
SSA New Media
3rd January, 2020

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment