Fadar mulkin Najeriya ta fitar da sanarwar da ke nesanta shugaba Muhammadu Buhari da hannu wajen gabatar da kudirin da ke shirin mayar da tsarin kowanne wa’adi na mulkin kasar zuwa shekaru 6, kudirin da ya sha kaye a gaban majalisun kasar cikin makon jiya.
Cikin sanarwar fadar ta bayyana cewa guda cikin ‘yan Majalisar wakilai da ta kira sunanshi da Mr John Dyegh ne ya gabatarwa Majalisar kudirin, kuma ko da majalisar ta aminta da kudirin ba zai fara aiki ba sai bayan gushewar gwamnati mai ci shekarar 2023.
A cewar babban mataimaki na musamman ga shugaba Muhammadu Buhari kan al’amuran da suka shafi Majalisa Senator Babajide Omoworare, ya bayyana cewa shugaban Najeriyar ya sha nanata rashin bukatar shi ta kara koda kwana guda a mulki bayan karewar wa’adinsa, hasalima ya sha alwashin kin mara baya ga kowanne dan siyasa yayin zaben shekarar 2023.
Kaii wlh nidai banji wani daɗiba ai yakamata ace tin awannan lokacin zai fara aiki sbd ai sabida shi aka buƙaci hakan pls susake nazar8 man
LikeLike