Gwamnatin Zamfara ta umarci Adamu Alieru da ya dawo da ₦biliyan 22

Gwamnatin jihar Zamfara ta nemi tsohon gwamnan jihar Kebbi, Sanata Adamu Aliero da ya mayar da kudade sama da Naira biliyan 22 asusun jihar wandaaka yi zargin an samu daga kamfaninsa-Allied Trading Firm- a matsayin kudaden kwangilar don hade garuruwa 75 da kauyukan kasa a 2013.


Kwamishinan ayyuka da sufuri na jihar, Engr. Isah Mayana, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a karshen taron majalisar zartarwa ta jiha a gidan Gwamnati dake Gusau.

Ya ce gwamnatin da ta gabata a karkashin tsohon gwamna Abdulaziz Yari ce ta ba da kwangilar ta sama da Naira biliyan 25.

Kwamishinan ya yi zargin cewa tun daga wannan lokacin, ci gaban ayyukan da kamfanin ya samu ya wuce kashi 60% kawai, don haka yazama dole gwamnatin yanzu ta gwamna Bello Mohammed Matawalle ta soke kwangilar.

Majalisar zartarwa ta jihar ta hada baki daya ta amince da soke wasu kwangilolin guda biyu ta Naira biliyan 27 kowannensu.

Su ne ayyukan samar da ruwan sha na karkara da aka bayar a shekarar 2013 ga Kamfanin Zongho na kasar Chana wanda ya sha bamban da kashi 13 da 75 cikin dari.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

3 thoughts on “Gwamnatin Zamfara ta umarci Adamu Alieru da ya dawo da ₦biliyan 22

  1. INA MUTUKAR KAUNAR ME DARAJA GWAMNA KUMA INAYI MASA FATAN ALHAIRI DA ADU,AR ALLAH DAFA MASA. NI KUMA ALLAH YA HADANI DASHI FUSKA DA FUSKA

    Like

Leave a comment