An yanka ta tashi a Jahar Zamfara

A yau alhamis 12-12-2019 kotun daukaka kara dake da zama a birnin tarayya Abuja (Court of Appeal) Ta yi watsi da karar da Hon Sani Takori Gummi ya yi in da yake kalubalantar hukuncin da (Supreme Court) ⚖️ ta yi na tabbatar da Hon (Dr) Bello Matawalle a matsayin zababben Gwamnan Jahar Zamfara da mataimakinsa da sanatoci 3 da ‘yan majalisar tarayya 7 da ‘yan majalisar Jaha 24.


Wannan kotun daukaka kara (Court of Appeal) ta yanke hukunci inda ta kara ta kara tabbatar da Hon Bello Matawalle a matsayin shine zababben Gwamnan Jahar Zamfara a karkashin jam’iyyar PDP da mataimakinsa da sanatoci da ‘yan majalisun Jaha da na tarayya.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

6 thoughts on “An yanka ta tashi a Jahar Zamfara

  1. Tabbas wannan shine nuna cewa Matawalle Zabin Ubangijine da Talakawa sika dare suna Rokon Allah akanshi Alhamdulillah.

    Like

  2. Allah yakarama takori yazo yabi gwamnati aje taredashi domin achiyar da jahar zamfara gaba zamfara sai DODO 4+4 INSHA ALLAH

    Like

Leave a comment