Gwamnan Zamfara zai gabatar da takarda a makarantar koyon ilimin tattalin arziki da ke London

Mai darajja gwamnan jahar zamfara, Hon. (Dr). Bello Muhammad Matawallen Maradun MON (Barden Kasar Hausa), zai gabayar da makala (takarda) akan abubuwan tattalin arzikin jahar zamfara musamman ta fuskar sashen hakar ma’adinai a makarantar nazarin tattalin arziki da ke London tsakanin ranakkun 2 ga watan December (watan 12) zuwa 5 ga watan December 2019.


Wannan na kunshe a cikin takardar goron gayyata mai dauke da sa hannu na hadin guiwa na shugaban zartaswa na kamfanin Lord’s Promotion Limited, Dr. Olesegun Okeowo, da kuma shugaban kamfanin Ankansas Consultancy, Ambassador Auwal Alhassan Gama kuma anka yi inkiyar ta zuwa ga mai girma gwamma.

A lokacin ziyarar, Ana sa ran mai darajja gwamna zai halarci wani taro akan ilimi da tsaro da kuma kalubale akan haka a jahar zamfara.

Mai darajja gwamna zai kuma tattauna da shugabannin zartaswa na makarantar koyar da ilimin tattalin arziki a ranar 2 ga watan December, 2019 inda ake sa ran za a kulla yarjejeniya a lokacin .

Har ila yau za a karbi bakuncin mai darajja gwamna zuwa halartar wata tattaunawa ta keke-da-keke a kebance da kungiyoyin ba da agaji na kasa da kasa a rana ta ukku ta wannan ziyara sannan daga bisani mai darajja gwamna zai hadu da kungiyar yan majalisar dokokin burtaniya domin tattaunawa da su.

Haka zalika za a karbi bakuncin mai darajja gwamna zuwa halarta wata tattaunawa da ma su ba da agaji domin sanya hannu akan wata yarjejeniya da za ta amfani al’ummar jahar zamfara.

YUSUF IDRIS GUSAU
Director General Press Affairs
Office of the Executive Governor,
Government House, Gusau.
16/11/2019

Fassarawa :

Ibrahim Bello Gusau Ibg
ZASMO Press Release Translation Committee.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment