Dole duk dan kwangilar da mu ka baiwa aiki ya yi shi kamar yadda mu ka umurta/Gov Matawalle

Domin tabbatar da dukkanin ‘yan kwangilar da aka baiwa aiki sun yi ayukkansu kamar yadda aka ba su, shi.


Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ya ziyarci titunan bayan tsohowar Tashar Gusau, Wanda gwamnatinsa ta Bayar da kwangila, haka zalika ya ziyarci titin babban masallacin Jumu’a na Gusau tare da takwaransa na Sabon Garin Gusau.

Gwamnan yana wannan ziyarar ne, domin ganin halin da aikin wadannan tituna ya ke tafiya.

Da ya ke jawabi a wajen wannan ziyarar Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ya bayyana Cewa dole ne duk wanda gwamnati ta baiwa aiki ya tabbatar ya yi, domin cigaban jahar. Hakan ne ma ya sa Mu ka zakulo ayukkan Titunan babban masallacin Jumu’a na Gusau tare da Takwaransa na Sabon gari Wanda tsohowar gwamnatin da ta wuce ta Bayar, Amma wadanda aka baiwa aikin su ka ki yi. Wanda yanzu Mu ke zagayawa domin ganin yadda ‘yan kwangilar ke gabatar da ayukkansu.


Gwamnan dai yana ziyarar ne, tare rakkiyar shugaban jam’iyar PDP na jahar Zamfara.

Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Executive Governor Of Zamfara State
16th November, 2019

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment