GWAMNATIN ZAMFARA TA YI BITA YI TARON AKAN SHA’ANIN TSARON JAHAR TARE DA MIKA MAKAMAI GA GWAMNATIN.

Tun bayan da mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Matawallen Maradun ya rika ragamar jagorancin jahar, ya ke ta biyar hanyoyin da su ka dace domin magance matsalar Tsaron Zamfara. Hakan ne ya sa gwamnan ya bullo da shirin sasanci Wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo zaman lafiya a jahar.

Sai dai abaya bayan nan ana samun ‘yan matsaloli nan da can daga bangarorin da ke gaba da juna.

Hakan ya sa gwamnatin ta jahar ta gayyato bangaren shuwagabannin ‘Yan sa-kai da tubabbun ‘yan bindiga Domin tattaunawa akan matsalolin da ke fusgowa a yanzu, tare da jin Abunda ya haifar da su da kuma hanyoyin magance su. Inda aka ji daga bangarorin biyu Kowane ya Bayar da shawara da kuma korafe-korafen da su ke da su. Tare karbar Makamai

Da Ya ke jawabi Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Hon. Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun. Ya yabawa gwazon shuwagabannin bangarorin biyu Akan irin goyon bayan da su ke baiwa wajen ganin an kawo karshen matsalar Tsaron Zamfara. Haka zalika ya yi kira ga dukkanin bangarorin su cigaba da Bayar da gudunmawa domin Kawo karshen matsalar, baki dayanta. Haka zalika ya nuna damuwa Akan masu cin amana Akan wannan sulhu daga dukkanin bangarorin. Don haka ya yi alkawarin daukar matakan da su ka dace domin maganinsu. Haka zalika Gwamnatin jahar Zamfara ta za rinka shirya taro wata-wata don yin bitar sha’anin tsaron Jahar da Sanin halin da ake ciki da kuma inda aka kwana. Don magance matsalolin da kan tusgo. Daga nan ya yi kira ga dukkanin bangarorin musamman Fulani da su Mika mukamansu ga gwamnatin domin a shirye take da taimake su Don ganin sun tsayu da Kansu.

Taron da ya samu halartar Mai baiwa gwamna shawara Akan sha’anin tsaro Hon Abubakar Dauran Justice, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jahar Zamfara da darakta Sss na jahar Zamfara da takwaransu na sojojin kasa. Da Sauran jagororin wadannan jama’a.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
11th November, 2019

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment