INNALILLAHI SUBHANALLAHI A’UZUBILLAHI, MASIFAR DA TA KUNNO KAI A CIKIN AL’UMMA, MADIGO!!!

INNALILLAHI SUBHANALLAHI A’UZUBILLAHI 

Masifar Da Ta Kunno Kai A Cikin Al’umma

MADIGO 

Daga fadila hikaya. 

Ba wani abu bane wannan face yawaitawar samuwar mata ‘yan madigo. Dole a kira wannan abin da masifa domin yana daga cikin abubuwan da ke haifar mana masifun da muke fuskanta a yanzu cikin al’umma.

Hakika wannan wata jarabawa ce da mata suka dorawa kansu, shin kina mace wacce za a kiraki da uwa ta yaya zaki fara aikata wannan mummunar abu haka? Shin wacce tarbiyya muke tunanin zamu dora yaranmu masu tasowa a kai nan gaba? Shin mun taba zama munyi tunanin wacce irin kalubalen rayuwa zamu fuskanta ta dalilin wannan aika aikar?.

Tabbas duk wacce ta samu kanta cikin irin wannan rayuwa ta hadu da jarabawa matuka. Haka ana cutar da iyayen yara ta jefa yaransu cikin wannan dabi’a ba tare da saninsu ba bayan sun riga sun basu ingantacciyar tarbiyya daga gida.wasu yaran kan jefa kansu da kansu ba tare da wani ya tilasta musu ba.

Mu sa ni a duk lokacin da muka kauce fadin Allah dole mu hadu da dana sa ni. Mu sa ni wannan dabi’a tana iya haifar mana da matsaloli kala kala kama daga ta gangar jiki har zuwa kwakwalwa, me yasa ba zamu bi hanyar da ta dace ba don samun biyan bukatar mu? Ko yarinya budurwa aka samu da wannan dabi’a bai dace da ita ba kasancewar ta mace da zaa kira ta da uwa watarana, balle macen da ke da igiyar aure a kanta.

Ya salam! Wallahi mata muji tsoron Allah, saboda mune kashin bayan gyara al’umma. Shin bama tuna makomar mu ne? Wace hujja muke da itada zamu bayar bayan mutuwar mu muna aikata wannan mummunar dabi’a ta madigo?

Wallahi haramcinta mai girmane. Saboda haka iyaye mata mu kula da mutanen da yaranmu ke mu’amala dasu ko a gida ko makaranta, mu zama masu matukar sa ido ga yaranmu wajen tafiyar da rayuwarsu na yau da kullum, haka iyaye maza su taimaka wurin ganin tarbiyyar yaransu bata gurbace ba ta dalilin wasu bata gari.

A k’arshe mu sa ni cewar dauwama a cikin wannan dabi’a ta madigo yana haifar da cuta a mahaifa, gaban mace wanda baya jin magani, sannan yana haifar da cutar mantuwa da tabuwar kwakwalwa, yana haifar mutuwar wulakanci ga duk me yinta. 

Ina kira ga iyaye maza da mata akan kulawa da tarbiyyar yaran da Allah ya basu amanarsu zai kuma tambayesu ranar gobe kiyama. 

MU JI TSORON ALLAH.

INNALILLAHI WA INNA ILAHI RAJI’UN,  MAHAIFIYAR NAFISA ABDULLAHI TA RASU. 

Mahaifiyar Nafisa Abdullahi Ta Rasu

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.

Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi tayi rashin mahaifiyarta yau Talata, kamar yanda ta bayyana, tace, mun rasa komai a yau amma Allah yafi mu sonki dan haka zamu biki da addu’a.

Nafisar ta kuma yi kira ga masoyanta da su saka mahaifiyar tata cikin addu’o’insu.

Sannan tayi Alkawarin fara lissafi daga yau har randa zata hadu da mahaifiyar tata a Aljannah, kamar yanda ta bayyana, Allah yasa haka.

Muna fatan Allah ya jikanta ya basu hakuri yasa Aljannah ce makomarta.

Hutudole

“AKWAI YIWUWAR BUHARI BA ZAI TSAYA TAKARA A 2019 BA, BABAGANA KINGIBE AKE MARARI”

“AKWAI YIWUWAR BUHARI BA ZAI TSAYA TAKARA A 2019 BA, BABAGANA KINGIBE AKE MARARI”

Muhammad Bin Ibrahim

14/08/2018

Binciken jaridar Daily Independent ya zaqulo cewa qasashen Tarayyar Turai, Amurka, da Ingila da Saudi Arebiya, sun matsa wa Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari lamba a kan kada ya sake tsayawa takara.

Wata majiya da jaridar ta kira sahihiya ta ce, an dau lokaci mai tsawo qasashen suna kira ga Buhari da bai kamata ya tsaya takara ba. Ban da dalilin rashin lafiyar Buhari da majiyar ta kawo, ta kuma qara da cewa tazarcen Buhari zai iya raba kan qasar.

Jaridar ta ce wani memban gudanarwa na jam’iyyar APC shi ma ya tabbatar da cewa, akwai yiwuwar Buhari ba zai yi takara ba. Ya ce don haka ma wasu ‘yan Buhariyya a fadar shugaban qasa suke ganin cancantar maye gurbinsa da Alhaji Babagana Kingibe, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya a zamanin Marigayi Umaru ‘Yar’aduwa. Amma ya ce har yanzu ba a tattauna batun a tsakanin ‘yan jam’iyya ba.

FALALAR KWANAKI 10, NA ZUHAJJ!!!  DAGA SHEAK ABDULHAKEEM AHMAD YA’AKUB GUSAU.

FALALAR KWANAKI 10, NA ZULHAJJ !!!

Sheak Abdulhakeem Ahmad Ya’akub Gusau 

Falalar Kwanaki 10, na Zulhajj, da Muhimmancinsu Abu ne, Wanda ba Sa6ani a ciki

Girman Wadannan kunaka yasa har Allah yayi rantsuwa dasu a Qur’ani Surutul Fajr aya ta 1

Imam Bukhari, Muslim, Tirmizi, Ibn Majah da Abu Daud duk sun ruwaito daga Ibn Abbas RA, cewa

Annabi saww, yace: Ba wasu Kwanaki da Allah yafiso ayi maSa baiwa a ciki, kamar Wadannan Kwanaki!

Sai Sahabbai RA, sukace: Koda zuwa Jahadi don Allah ya Manzon Allah??

(Sai Annabi saw yace:) sai dai mutumin da ya fita da rayuwarsa da dukiyarsa bai dawo da komi ba

(Wato sai dai Wanda yasamu Shahada ne, kadai yafi daraja ga Wanda yayi ibada Wadannan Kwanaki)

A riwayar Tirmizi, Ibn Majah da Albaihaqi, daga Abu Huraira RA, daga Annabi saww yace:….

Kowane Azumin kowane wuni na Zulhajj yana dai dai da Azamin Shekara, hakama raya kowane dare da ibada, na dai dai Lailatul Qadri 

A takaice, ana bukatar raya watan dukkansa da ibada da nisantar dukkan sa6on Allah, Musamman kwana 10, na Farko

IRE_IREN IBADU DA AKE SO AYI:

1. Azumin dukkan ranakunsa

2. Raya dukkan dararensa

3. Saukar Qur’ani inzai yiwu

4. Ciyarwa ga Mabukata

5. Shayarwa ga Mabukatata

6. Suturtarda Mabukata

7. Kiyaye Sallolin Farilla a Jam’i

8. Yawaita Sallolin Nafila

9. Nisantar dukkan Sa6o

10. Yawaita Zikrori, Tasbihi, Takbiri, Tahmidi da sauransu

11. Salati da Istigfari

12. Da duk abinda Allah keso na ibada Magana da aiki

Wanda kuma zai yi Layya tunda watan ya kama, bazaiyi Aski ba, ko Saisaye da kuma yanke Kumba/Farce/Akaifa

Kamar yadda yazo a Had is in Ummu Salma, daga Annabi saww

Abdulhakeem Ahmad Ya’akub Gusau, Zulhajj 1439AH_2018

DABBOBIN LAYYA DA KWANAKI 10 NA FARKON ZUL-HAJJI. 

DABBOBIN LAYYA DA KWANAKI 10 NA FARKON ZUL-HAJJI. 

Fassarar Salihu Makera

Copy Jaridar Aminiya. 

Daga Hudubar Imam Murtada Muhammad Gusau

Babban Limamin Masallacin Nagazi-Ubete, Okene, Jihar Kogi. 

Mukaddima:

Bayan haka ya bayin Allah! Daga cikin muhimman lokuta na yin ibada akwai ranaku 10 na farkon watan Zul-Hajji – wata na 12 na shekarar Musulunci, wadanda Allah Ya fifita a kan sauran kwanaki na shekara.

Ibn Abbas (RA) ya ruwaito cewa: “Annabi (SAW) ya ce: “Babu wani aiki da ya fi alheri irin wanda aka yi a ranaku 10 na farkon Zul-Hajji.” Sai wadansu sahabbai suka ce: “Ko da jihadi a tafarkin Allah?” Sai Annabi (SAW) ya ce: “Ko da jihadi a tafarkin Allah, sai dai in mutum ya tafi da ransa da dukiyarsa bai dawo da komai ba.” (Buhari). 

Wadannan kwanaki goma manya ne kuma mafiya soyuwa ne a wurin Allah. Ibn Umar (RA) ya ruwaito cewa: “Annabi (SAW) ya ce: “Babu wasu ranaku da suke da girma kuma suka fi soyuwa a wurin Allah fiye da wadannan kwanaki goma na farkon Zul-Hajji, don haka ku yawaita tahlili (La’ilaha illallah) da takbiri (Allahu Akbar) da tahmidi (Alhamdulillah) a cikinsu” (Musnad Imam Ahmad), kuma Sheikh Ahmad Shakir ya inganta shi.

Daga cikin darajojin da wadannan kwanaki goma suke da su akwai cewa:

1- Allah Yana yin rantsuwa da wani abu domin Ya nuna muhimmancinsa, kuma Allah Ya yi rantsuwa da wadannan ranaku goma a cikin Alkur’ani Mai girma inda ya ce: “Ina rantsuwa da alfijiri. Da darare goma.” (k:89:1-2).

Malamai magabata da suka hada da Ibn Abbas (RA) sun ce wadannan darare goma da aka ambata a cikin Alkur’ani su ne darare goma na farkon Zul-Hajji.

2- Annabi (SAW) ya ce wadannan darare goma su ne ranaku mafiya alheri na shekarar kamar yadda muka ambata a Hadisi na baya.

3- Su ne ranaku mafiya alheri na yawaita ambaton Allah, kamar yadda Hadisin da ya gabata ya nuna.

4- Sun kunshi Ranar Arfa (9 ga Zul-Hajji) wanda a cikinta Allah Ya cika wannan addini. Kuma yin azumi a cikin wadannan ranaku yana kankare kananan zunuban shekarar da ta gabata da shekarar da ake ciki, (manyan zunubai suna bukatar tuba da mayar da hakki ga mai shi). 

5- Sun kunshi “Ranar Hajji Mafi girma” wato ranar Idin Layya (10 ga Zul-Hajji), kuma wannan rana ita ce rana mafi girma a daukacin shekara.

Don haka ku yawaita karatun Alkur’ani a cikinsu, ku yi sallolin nafila da kiyamul Laili da sadaka da yada ilimi da tuba ga Allah. Ku yawaita neman gafara ta fadin Astagfirullah, ku yi azumi da jikinku, ma’ana ku kaurace wa haram ko fadin haram ko sauraren haram da sauransu, kuma ku yi addu’o’i ga al’ummar Musulmin duniya.

’Yan uwa maza da mata! Ku yi gaggawar ribatar wadannan ranaku kafin lokaci ya kure muku.

Ya bayin Allah! A yau aikin da ya fi hada dukan Musulmi, matasa da dattawa, maza da mata, bakake da farare, kuma yake kawo farin ciki a fuskar kowa, shi ne ibadar Layya. Layya ibada ce ta sadaukarwa ta hanyar yanka dabbobi domin neman yardar Allah. Ana yin ta ce domin tunawa da wani muhimmin abin tarihi da ya auku a lokacin da Allah Ya umarci Sayyidina Ibrahim (AS) ya yi layya da dansa Sayyidina Isma’il (AS), kuma a lokacin da yake shirin aiwatar da umarnin Allah, sai Allah Ya musanya masa da rago wanda Sayyidina Ibrahim (AS) ya yanka.

Sayyidina Ibrahim (AS), ya ci jarrabawa, domin ya shirya don yanka dansa saboda bin umarnin Allah.

 Abokaina yanzu kuna jin wahalar ku yi layya da dabba (ta amfani da kudinku) don bin umarnin Allah? Bai kamata ni da ku mu kasa cin wannan jarrabawa ba, domin duk wanda yake da hali ya yi layya a madadin iyalinsa.

’Yan uwa maza da mata! Za a iya yanka Layya a kowane lokaci bayan Sallar Idi har zuwa faduwar rana ta uku a bayan Ranar Idin. Wannan na nufin wuni hudu (wunin Idi da karin wuni uku bayan Idi). Kamar yadda Imam Shafi’i (Rahimahullah) ya nuna. Amma a fahimtar sauran manyan malamai: Abu Hanifah da Malik da Ahmad, ana yin layya ce a cikin wuni uku. A fara da ranar Idi a kare a wuni na biyu bayan wunin Idi lokacin faduwar rana.

Ana iya yanka Layya da rana ko da dare, matukar dai a cikin wadannan ranaku ne, amma yin ta da wuri (jim kadan bayan Sallar Idi) ya fi.

Sunnar Layya ita ce a raba naman uku, kuma ba tilas ba ne a raba daidai-wa-daida. daya a raba ga talakawa da mabukata, dayan a bar wa iyali da makwabta da dangi da abokai, dayan kuma ka yi yadda ka so da shi.

Layya Sunnah ce mai karfi a kan kowane Musulmi mai hali. Wannan shi ne ra’ayin akasarin malamai. Amma a wurin wadansu malaman wajiba ce a kan Musulmin da zai iya. Kuma tana daya daga cikin kyawawan ayyuka a Musulunci kamar yadda A’isha (RA) ta ruwaito daga Annabi (SAW) cewa: “dan Adam bai taba yin wani aiki a Ranar Layya da ya fi soyuwa a wurin Allah ba, kamar zubar da jinin dabba (yankan Layya).”

Galibin malamai sun ce yanka Layya ya fi alheri da yin sadaka da kwatankwacin kudin abin abin yankar.

Ya ’yan uwa! Ana yin Layya ce da dabbobin gida wato shanu da rakuma da tumaki da awaki. Kuma yanka ragoko tunkiya da bunsuru ko akuya ya fi falala a kan sauran dabbobi, saboda Annabi (SAW) bai taba yin Layya ba face da wadannan dabbobi. Amma ana iya yanka rakuma da shanu lokacin Layya. Kuma wajibi ne abin yankar ya kasance lafiyayye, kosasshe da za a iya cin namansa kuma a yi ta a matsayin ibada ga Allah kamar yadda Allah Ya ce: “Kuma wanda ya girmama ibadojin Allah, to lallai ne ita (girmamawar) tana daga ayyukan zukata na takawa.” (k:22:32).

Kuma wajibi ne rago ko tunkiyar su haura wata shida kamar yadda Ibn Majah ya ruwaito cewa sai Jaza’a za a yi Layya da ita. Ga jinsin akuya wajibi ne ya kai shekara daya, sannan saniya shekara biyu, shi kuma rakumi shekara biyar. Kuma kada a yi Layya da nakasasshiyar dabba, kamar mai ido daya ko marar lafiya ko gurguwa da nakasar ta bayyana ko ramammiya marar nama ko marar mai kamar yadda Buhari ya ruwaito daga Barra’u bin Azib daga Annabi (SAW).

Kuma mafi yawan malamai sun tafi a kan cewa siffofi hudu da aka ambata a Hadisin za a iya amfani da su wajen hukunci kan duk wata nakasa. Don haka duk wata nakasa da ta kai ta ko ta fi ta ba za a yi Layya da dabbar ba, kamar makauniya ko marar kafa ko gurguwa.

Kuma ana iya Layya da dabbar da aka dandake, saboda Annabi (SAW) ya yi haka, haka dabbar da aka haifa ba ta da jela ko take da rabinta, amma wadda aka yanke jelarta duk ba za a yi Layya da ita ba.

Sannan tunkiya ko akuya daya ta wadatar mai gida ya yi Layya da ita ga kansa da iyalansa. Kuma ya halatta mutum bakwai su yanka saniya ko rakumi daya a matsayin layyarsu. Kamar yadda Jabir bin Abdullahi (RA) ya ruwaito cewa Annabi (SAW) ya yi haka a shekarar Hudaibiyya. (Muslim ya ruwaito).

Kuma mai yin haka zai iya hadawa da iyalinsa a cikin ladar domin a nan daidai yake da mai yanka tunkiya ko akuya.

Kuma bai halatta a yanka Layya kafin a yi Sallar Idi ba, duk wanda ya yanka Layya kafin Sallar Idi ya yanka wa iyalinsa naman ne kawai sun ci amma ba Layya ya yi ba, kamar yadda Annabi (SAW) ya nuna. Kuma idan mutum zai yanka layyar ya ambaci sunan Allah, ya ce: “Bismillah, Ya Allah, wannan daga rahamarKa ce kuma dominKa ne.”

An fi so mutum ya yanka Layyarsa da kansa in ba zai yi haka ba, to ya halarci yankar, sannan ya raba uku kamar yadda muka ambata a baya. Ya ci rubu’i daya shi da iyalinsa, ya bayar da daya rub’in sadaka, dayan kuma ya yi kyauta da shi, kamar yadda Annabi (SAW) ya shaida wa ’yarsa Fatima (RA) cewa: “Ki kasance a lokacin da ake yanka Layyarki. Allah Yana gafarta miki a lokacin digar farko na jininta.” (Baihaki da Abdul Razzak suka ruwaito).

 Hikimar Layya:

1 – Neman kusanci ga Allah ta hanyarta.

2 – Raya Sunnar Shugaban Masu Tauhidi Annabi Ibrahim (AS) wanda Allah Ya umarce shi ya yi Layya da dansa Annabi Isma’il (AS) sannan daga baya ya musanya shi da rago, kuma Annabi Ibrahim (AS) ya yanka shi a madadin Annabi Isma’il (AS) din.

3 – Yalwatawa da kyautata wa iyali a Ranar Idi.

4 – Fadada jin dadi a tsakanin matalauta da mabukata ta hanyar ba su sadakar naman Layya.

5 – Yin godiya ga Allah kan yadda Ya hore mana dabbobin ni’ima.

Abubuwan da wanda ya yi niyyar Layya zai guje musu:

Idan mutum ya yi niyyar zai yi Layya to da zarar wata Zul-Hajji ya kama ba zai yi aski ko ya yanke farce ba har sai ya yanka abin Layyarsa.

Muslim ya ruwaito a cikin Sahihinsa cewa Ummu Salma (RA) ta ce, Annabi (SAW) ya ce: “Idan kuka ga jinjirin watan Zul-Hajji kuma dayanku yana da niyyar yin Layya, to kada ya aske gashinsa ko ya yanke farcensa.” (Muslim).

Haka kada a biya ladan mai gyara naman Layya daga abin Layya. Domin Aliyu bin Abu Talib (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya umarce ni da in lura da Layyar wani rakumi, in bayar da namansa da fatarsa a matsayin sadaka kuma kada in bayar da komai daga cikinsa ga mahauci a matsayin ladan aikinsa. Ya ce, “Zan iya ba shi wani abu daga abin da na mallaka.” (Muslim).

’Yan uwa maza da mata! Ina rokon Allah Madaukaki ya amsa min da ku da sauran Musulmin duniya, kuma Ya sa dominSa kadai muke yi. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da sahabbansa. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

Ya Allah! Ka taimake mu wajen rayuwa bisa koyarwar Alkur’ani da Sunnah. Ya Allah Ka nuna mana gaskiya Ka ba mu ikon bin ta, kuma Ka nuna mana karya Ka ba mu ikon guje mata.

Ya Allah! Ka shiryar da mu, Ka kare mu daga ayyukan jahilci da barna. Ka kare mu daga gazawarmu. Ka sanya karshen ayyukanmu su kasance mafi alherinsu da dacewarsu. Kuma Ka gafarta mana Ya Ubangiji.

Ya ’yan uwa! Duk abin da na fadi mai kyau a Huduba ta yau daga Allah Madaukaki ne, kuma duk wani kuskure daga gare ni kuma muna neman tsarin Allah daga bayar da muguwar shawara da dukan barna da fitina. Kuma ina rokon Allah gafara idan na ketare iyaka a cikin duk abin da na ce ko na aikata.

Godiya ta tabbata ga Allah, Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Manzon Allah da alayensa da sahabbansa.

Ina kammala wannan Huduba ina mai rokon Allah Madaukaki Ya gafarta mana zunbunamu. Ku nemi gafararSa, Lallai Shi Mai gafara ne Mai jin kai.

Imam Murtada Muhammad Gusau, Babban Limanin Masallacin Juma’a na Nagazi-Ubete da Masallacin marigayi Alhaji Abdurrahman Okene da suke Okene Jihar Kogi. Za a iya tuntubarsa ta tarho: +2348038289761.

FALALAR RANAR JUMU’AH 

FALALAR RANAR JUMU’AH

Ranar Juma’a rana ce mai falala da girma, wannan ya sa Manzon Allah (Sallallahu Ailaihi Wa Sallam) yake girmamata, yake kuma ware ta da Karin wasu Ibadoji na daban, ga kadan daga abubuwan da ranar Juma’a ta kebanta da su:

1. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya kasance yana karanta Suratus Sajada da Suratul Insan a duk asubar ranar Juma’a, kamar yadda Imamu Muslim ya rawaito.

Shaikhul Islam Ibni Taimiyya yana cewa “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) yana karanta wadannan Surori ne saboda sun kunshi abin da ya faru, da ma abin da zai faru a wannan ranar, kuma Surorin suna dauke da bayanin halittar (Annabi) Adam, da ambaton makoma (lahira) da (bayanin) abin da zai faru ga bayi (a lahira), duk wannan zai faru ne a ranar Juma’a……..” (Duba “Zadul Ma’ad” (1/364).

2. Mustahabbi ne a yawaita salati ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) a daren wannan rana, da yininta, saboda fadin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) “ku yawaita yi min salati ranar Juma’a da darenta” (Baihaki ne ya rawaito shi).

Imam Ibnil Kayyim yana cewa “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) shi ne shugaban halitta, ranar Juma’a kuwa ita ce shugabannin ranaku, don haka yin salati ga Manzon Allah (Sallallahu Aliahi Wa Sallam) a wannan ranar yana da fifiko akan sauran ranaku…….” (Zadul Ma’ad) (1/364).

3. Yin sallar Juma’a da halartata yana daya daga cikin maya-mayan taruka na Musulunci, don haka ma duk wanda ya ki halartar Juma’a da gangan to Allah zai rufe masa zuciya, alheri ba zai rika shigarta ba.

4. Yin wanka acikinta.

5. sanya turare, an karbo Hadisi daga Abu Sa’id ya ce “Wankan Juma’a wajibi ne akan duk wani baligi, sannan ya yi aswaki, ya sanya turare in ya samu” Bukhari ne ya rawaito shi Hadisi na (880).

6. Mustahabbi ne yin aswki a wannan ranar, kamar yadda ya gabata a Hadisi.

7. Zuwa Masllaci da wuri.

8. Shagalta da sallahr nafila da Zikiri, kamar karatun Alkur’ani har zuwa fitowar liman.

9. Wajibi ne a saurari Huduba, da yin shiru ya yin da ake yinta.

10. Karanta Suratul Khahfi a wannan rana, saboda fadin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) “Duk wanda ya karanta Suratul Khahfi a ranar Juma’a, wani haske zai daga daga karkashin kafarsa har zuwa kololuwar sama, zai zamar masa haske ranar alkiyama, kuma za a gafarta masa abin da yake tsakanin Jumu’o’in guda biyu”.

Hakim da Baihaki ne suka rawaito shi (Shiekh Albani ya ingantaa wanan Hadisi a cikin :Irwa’ul Galil” (3/93).

11. Ana so a karanta Suratul Juma’a da Suratul Munafikun, ko kuma Suratul A’ala da Gashiya ya yin Sallar Juma’a.

12. Rana ce ta idi ga Musulmi, wanda yake maimaituwa duk sati.

13. Mustahabbi ne a sanya kaya kyawawa, saboda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Ssllam) yace

“Duk wanda ya yi wanka ranar Juma’a ya sa turare-in ya samu-sannan ya saka kyawawan tufafina, ya fita cikin nutsuwa, har ya isa Masallaci, ya yi nafila gwargwadon abin da yaga dama, bai cutar da kowa ba, sannan ya yi shiru har liman ya fito ya yi Sallah, to hakan ya zama masa kaffarar abin da ke tsakanin Jma’a biyu” Imamu Ahmad ne ya rawaito wannan Hadisi.

14. Mustahabbi ne a gyara Masallaci asa masa turare. Umar Dan Khaddab (R.A.) ya yi umarni a lokacinsa a rika sawa Masallacin Madina turare a duk ranar Juma’a bayan rana ta raba.

15. Baya halatta ayi tafiya a ranar Juma’a, kafin ayi Sallar Juma’a in dai lokacinta ya shiga. Amma idan lokacin bai yi ba, to malamai sun yi sabani akan hakan. Sai dai zance mafi rinjaye ba laifi a tafi Duba “Almugni” na Ibnu Kudama (3/248). Da “Zadul Ma’ad” (1/370).

16. Ranace da ake son yawaita yin Ibada a cikinta, kamar yawaita Salati ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam), Zikiri, nafilfilu, karatun Alkur’ani da sauransu.

17. Yin sadaka a wannan rana daban yake da yin ta a sauran ranakun sati, kamar yin sadaka ne a cikin watan Azumi.

18. Ranace da Allah ya yi wa wannan al’umma kyautar ta kamar yadda Hadisi ya nuna (Duba Za’dul Ma’adi (1/40).

19. Rance da ba a kebance ta da Azumi, sai dai in mutum zai hada ta ranar Alhamis, ko Assabar.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce “ka da dayanku ya yi Azumin ranar Juma’a, sai in ya Azumuci ranar da take gabaninta ko bayanta” (bukhari da Muslim ne suka rawaito).

20. Haramun ne saye ko sayarwa ga wanda ya ji kiran Sallahr Juma’a, lokacin da liman ya hau Mimbari. Idan kuwa an kulla ciniki a wananan lokaci, to malamai sun yi sabaani a kan ingancinsa. Imam Khurdabi da Ibnu kasir sun rinjaya rashin ingancinsa, don haka ya zama lalatacce (Duba Tafsirin Khurdubi (18/96) da Tafsirin Ibnu Kasir (4/392).

Muna Rokon Allah ya bamu ladan dukkan ibadun da zamuyi a cikin wannan rana mai albarka.

GAREKU MANIYATAN HAJJIN BANA NA JAHAR ZAMFARA

GAREKU MANIYATAN HAJJIN BANA NA JAHAR ZAMFARA

Ana kira ga Maniyyatan kananan Hukumomin Bungudu da Bukkuyum da Kaura Namoda da Tsafe da Zurmi da su Halarta a sandanin alhazzai dakr samuru dake garin Gusau. 

A yau da misalin karfe 6:00㏘ na marecen domin shirye shiryen wucewa kasa mai sarki saudi arebiya. 

Sanarwa Alh. Abubakar Spawa Dambo, Shugaban Hukumar Aikin Hajji na Jahar Zamfara.

BUƊAƊƊIYYAR WASIKA ZUWA GA TSOHON GWAMNAN ZAMFARA KUMA SANATA A YANZU! 

BUƊAƊƊIYYAR WASIKA ZUWA GA TSOHON GWAMNAN ZAMFARA KUMA SANATA A YANZU! 

Daga Nura Mai Apple, Gusau.

Assalamu alaikum, bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci, babu shakka, zan yi farin ciki matuƙa idan wannan wasiƙa tawa ta same ka a cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali a duk inda kake a cikin Faɗin Ƙasar nan.

Haƙiƙa zan yi amfani da wannan damar domin rubuto maka wannan wasikar da zimmar son samar da sauyin da muka daɗe muna dako a cikin jihar Zamfara. Ya Mai girma Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, kasancewarka ɗan asalin jihar Zamfara kuma wanda tun fal-azal yake da muradin ganin jihar ta ci gaba da kowane fanni, wanda sanadiyar haka ne ma ya saka har ka kwaɗaita da son kafa shari’ar Musulunci a jihar Zamfara, kuma ka samu nasarar haka tun a can lokacin gwamnatinka, kuma duk wani talaka, da shugabanni, da iyayen mu sarakuna, da sauran masu madafun iko, duk suka yi maka mubayi’a. Kuma suke daukar ka Shugaba mai matuƙar muhimmancin gaske a tarihin wannan jiha. Inda har ta kai babu wanda ya isa ya nuna maka ɗan yatsa a duk cikin jihar mu ta Zamfara a sakamakon darajantawa da al’ummar jihar Zamfara suke yi izuwa gare ka.

Ya mai girma Sanata, wannan kwarjinin dake a kwai a tare da kai, har ya saka duk wani mai son wata kujerar madafar iko a jihar Zamfara sai yayi kamun ƙafa a wajan ka, hasali ma duk wani mai riƙe da wani muƙamin siyasa a Zamfarar (a yanzu) yana da alakar tasowa a karkashin ka ne, kuma duk yadda kace haka ake suke aiwatarwa ba tare da yi maka jayayya ba. A hannu daya kuwa, haka ma, ko a can babban birnin tarayya Abuja kana daga cikin waɗanda suke da ƙarfin faɗa a zauren Majalisar Dattawa.

To amma wannan karfin fada aji naka, bai sa kayi yunkurin bayyana matsalolin dake addabar al’ummomin wannan jiha ba. Hakiƙa kasancewar ka babban mutum kuma mai son Addinin musulunci, kuma wanda ake yiwa lakabi da “Limamin Chanji” haka ma “Jagoran Siyasa a Zamfara” kuma “Kwamandan Gwamnatin Addinin mu Al’ummar mu” ya kamata kawo yanzu, kace wani abu akan kisan gillar da ake yiwa al’ummar jihar Zamfara.

Mai Girma Sanata, ya kamata don Allah kace wani abu mana koda a can cikin zauran Majalisa ne, da nuna rashin jin dadin ka akan abubuwan dake faruwa a Zamfara. Wallahi duk wanda yaga halin da ‘yan uwanmu ‘yan gudun hijira suke ciki a sassan yankuna na Zamfara zai yi matuƙar zubar da hawaye haɗi da tausayin irin halin da suke ciki na rashin kyawon matsogunni haɗi da kewar yankunansu inda sunka baro badon suna so ba.

Ya mai girma Sanata, cike da Ladabi da girmamawa nake ƙara tuna maka da cewa bayan kisan gillar da aka yiwa ilahirin wasu yankunan jihar Zamfara, al’ummar yakin da kake wakilta na karamar hukumar Anka yayi matuƙar girgiza al’ummar Jihar Zamfara dama ƙasa baki daya. Bayan kuma wanda ya faru na baya-bayan nan a ƙaramar hukumar Maradun, inda yanzu haka ‘yan gudun hijira suke jibge ruwa suna dukansu saboda rashin cikakken galihun da suka rasa. 

Zamfara gaba daya har yanzu babu wani kason kudi na musamman da aka ware domin kawai kula da ‘yan gudun hijira bayin Allah talakawa marasa galihu, dalilin wannan ne ma yasa har yanzu mun rasa wasu ƙungiyoyin ƙasa-da-ƙasa, ko na nan cikin Najeriya da suka zo nan Zamfara domin bayar da wani tallafi ga ‘yan gudun hijirar. Ya kamata gwamnatin jihar Zamfara ta samar da Sansanin ‘yan gudun hijira a hukumance domin bayar da taimakon gaugawa ga al’ummar Zamfara gaba ɗaya wadanda wannan lamarin ya shafa. Domin hakan zai matuƙar rage wahal-halun da suke fama da su, na ƙunci kamar rashin abinci da sutura, ga kuma uwa-uba rashin matsuguni. 

Ya mai Girma Sanata, Duk a lokacin Damina akwai wasu cututtuka masu yaɗuwa a cikin al’umma a Zamfara kamar su; Ƙwalara (Amai Da gudawa), kuma wannan yana faruwa sanadiyar rashin kyawun tsabtar muhalli, to ballantana ace dubbannin mutane suna rayuwa a cunkushe babu fasali irin na walwalar dan adam.  

Da wannan nake ganin kamar zafin radadin wannan al’amarin ya ta’azzara. Wadanda ke fama da yunwa, ina zancen tsabta a gare su? Ke nan rayuwar wadannan bayin Allah tana cikin halin ni-‘ya-su.

Ya kamata Mai Girma Sanata Yarima, ka fito ka bayyana wa masu riƙe da madafun ikon jihar nan da su yiwa talaka adalci, ga jagorance su, kuma ka tilasta yin hakan, domin dukkanin su masu biyayya ne izuwa gare ka. Domin kuwa, yin hakan zai sa a samu a gudu tare kuma a tsira tare. Kasancewar zaman lafiya yafi komai daɗi kuma sai da zaman lafiyar ne arzikin jiha yake faɗaɗa har kowa ya himmatu wajen neman na kan sa, har ya kasance talakawa sun samu abin rufa wa kansu asiri cikin walwala. Babu ƙasar da za ta ci gaba a duniya matuƙar babu zaman lafiya da kwanciyar hankali da kaunar juna. 

A ƙarshe ina amfani da wannan damar wajan yin addu’ar samun zaman lafiya mai ɗorewa a jihar Zamfara da Najeriya baki daya.

Daga: Nura Muhammad Mai Apple Gusau, ɗan kishin Marasa galihu kuma ɗan ƙungiyar Muryar Talaka Ta Ƙasa Reshen jihar Zamfara 08133376020.

KO KUNSAN MACEN DA TAFI KOWACE MACE TSAFTA A DUNIYA 

KO KUNSAN MACEN DA TAFI KOWACE MACE TSAFTA A DUNIYA.

fb_img_1533297921607-267613622.jpg

BINCIKEN MASANA DAGA KASAR AMRUKA.

Mace Musulma Ita Ce Ta Fi Tsafta A Duniya

Batun sha’anin tsafta yana daga cikin muhimman abubuwan da ake fatan gani a wurin ko wace ‘ya mace saboda yanayin halittar da Allah ya yi musu. Ba kamar namiji ba, a duk wata mata suna fitar da jini (wadanda suka isa haila), sannan ga batun abin da ya shafi haihuwa da raino da sauran su.
A wannan makon mun yi muku nazari kan yadda wani bincike ya gano cewa mace Musulma ita ce mafi tsafta a duniya saboda tsarin da Musulunci ya kawo musu tsakanin sabon aure da idda. Matar da mijinta ya sake ta, ya kamata ta jira a kalla wata uku, haka ma matar da mijinta ya mutu ya kamata ta jira a kalla wata hudu da kwana 10 kafin ta yi wani auren. Idan kuma ta kasance tana da ciki , to za ta jira har sai ta haifi yaron.

Wannan abu yana ba wa kimiyyar zamani mamaki bayan cewa tuntuni wannan ilimin a kwai shi cikin addinin Muslinci. Idan muka duba zamu ga cewa a cikin halittar maza da kuma mata za mu ga akwai bambanci sosai. Idan namiji ya auri mace sai ya zo ya sake ta, to wannan zai saka ta fada cikin damuwa.

Wannan zai haifar mata da rashin natsuwa, kuma zai kawo mata damuwa mai tsanani. Kimiyya ta tabbatar da cewa bayan sakin aure, a hailar farko ta mace tana jinin da ya kai kashi 32 zuwa 35 daga cikin dari. Haka ma a haila ta biyu tana jinin da ya kai kashi 67 zuwa 72, cikin na uku kuma tana jinin da ya kai kashi 99.9 daga cikin dari.
Bayan haila ta uku, yana wanke wa mace mahaifarta tare da samun jini mai tsafta. Saboda haka, yin karuwanci ga mace ko kuma kwanciya da namiji fiye da daya yana kawo cututtuka a mahifa saboda haduwar maniyyi.
Yana da kyau macen da aka saka ta jira, domin zai kawu masalaha. Saboda jiran zai saka sabanin da aka samu kowa zai huce. Shi ya sa Allah S.W.T ya ce, mata su jira har na tsawon wata hudu da kwana goma. Lokacin zai sa duk wani fushi da ma’aurata suka yi, za su huce kuma za su iya gyara tsakaninsu.
Wannan al’amari shi ya sa masana daga Amruka suka yi bincike a cikin kasashe Musumi na Afirka. Sun gano cewa matan Musulmi suna auren namiji daya ne, sannan binciken ya gano cewa matan da ba Musulmai ba, suna kwanciya da namiji fiye da daya, daga biyu zuwa uku.
Wannan ya sa suka gano cewa addinin Musulinci, shi ne kadai addinin da ke tabbatar da kare mata da kuma al’umma gaba daya. Saboda haka matan Musulmai sun fi tsafta a duniya baki daya.

AIKIN HAJJI A SAUKAKE

AIKIN HAJJI A SAUKAKE!

Da Sunan Allah, Salati da Sallama su tabbata ga Manzo da Iyalansa da Sahabbai.

Sheak Abdulhakeem Ahmad Ya’akub Gusau.

image

Kasancer aikin Hajji, ba rana daya akeyinsa ba

Don haka zanyi bayanin dai dai da ranakun aikin:

RANAR 8, GA WATA

Ana fara aikin Hajji ne, ranar takwas ga watan Zulhajj, ana karanta (Yaumu Tarwiyati)

A wannan rana mai Hajjin Tamattu’i, zai daura Harma da Hajji da Hantsi

1. Zaiyi wanka, da duk abinda yayi lokacin Umra

Na gusar da gashi, cire kumba, daura Harami da sauran su

2. Zai yi niyya da Hajji, kamar yadda lokacin Umra, illah a wannan Niyar Hajji zai yi

Zai CE: Labbaika Hajjan, bayan kuma yayi Niya a zuciya

Ko Nawaitul Hajja Wa’ahramtu bihi lillahi Ta’alah

Idan yakara da: Rabbana Taqabbal miniy ba komi

3. Daga za’kawo motoci a daukeku zuwan filin Mina

Za’atafi ne, ana Talbiya(Labbaikallahumma Labbaik…)

4. An so zuwa filin Mina kafin rana ta karkata,(Zawwal)

Idan an sa6a dai ba komi, amma dai a yawaita Talbiya

5. Za’ayi Sallolin Azuhur da La’asar da Magrib da Isha’i

Sai dai Azuhur da La’asar da Isha’i kowace raka’a 2, amma a lokacin ta

6. Za’a kwana anan har gari ya waye, rana ta fito, sai a tasamma arafa

RANAR 9, GA WATA, WUNIN ARFA

A Wannan rana ne, ake tsayuwar Arfa

1. Za’a tafi ana Talbiya har a isa a cikin filin Arfa

Idan akaje Arfa, anso a sauka Namira, idan yayiwu, inbai samuba duk Inda ka tsaya yayi

Sai dai wurinda ake kira da (Badni Uranata) ba’atsuya nan

2. Idan rana ta karkata (Zawwal)
za’ayi Sallolin Azuhur da La’asar tare

Za’ayi su a jam’i, kowace raka’a 2, kiran Sallah 1, ikama 2

Anso a saurari Khuduba daga Limamin arfa, don jin hukunce hukuncen Hajj

Daga nan tsayuwar Arfa zata fara, har faduwar rana

3. Tsayuwar Arfa, na nufin kasancewar Alhaji a filin Arfa, ana addua da zikrori

Daga karkatawar rana zuwa faduwarta, a tsaye ko zaune koma kwance

Koda mutum baya lafiya, yazo filin yazauna koda baisan ankawo shi ba, tsayuwarsa tayi

Ko rana ta fadi, mutum bai zo Arfa ba, bata kubce masa sai alfijir ya hudo

Ana son yawaita addua fiyeda ko’ina, da tuba da kuka da kastastarda kai ga Allah

Yazo a Hadisi, yana cikin mafi girma Zunubi mutum yayi tsayuwar
Arfa yayi tunanin ba’a Gafarta masa.

Mafi girman abinda Annabi saw ya fada da sauran Annabawa bayan addua, shine

La’ilaha lllallahu wahdahu lasharika lahu lahul mulku, walahul hamdu wahuwa alah kulli sha’in, Qadirun

Kuma anfi so Alhaji kar yayi Azumi, don jin kafin tsayuwar arfa, ba za’ayi Magri da Isha’a filin arfa ba.

ZUWA MUZDALIFA:

1.Bayan faduwar rana ana filin Arfa, da sharadin a tabbata ta fadin

Daga nan, sai a tasarwa filin Musdalifa cikin cikar nazuwa, ba ture_ture

Amma yanzu dayake ana daukar Alhazai ne da motoci, to sai su Kira

Koda andade ba’a kawo mota ba, ko andade ba’a kwashe kuba ba komi

2. Ba za’ayi Sallolin Magriba da Isha’i, ba sai can koda lokaci yatafi

3. Abubuwan da zakayi a filin Muzdalifa:

Ya tabbata ya shiga cikin filin Arfa, kafin ya ajiye kayansa, akwai alamomi

*A fara yin Salloli kafin komi, dazarar an isa

Kuma za’ayi Magriba raka’a 3, Isha’i raka’a 2, Jam’i lokaci 1, kiran Sallah 1, Iqama 2

* Ya nemi abinci yaci idan yana bukatar haka

* Ya kwanta da wuri yayi bacci, don aikin dake gabansa gobe

Wajen baccin ba’arufe kai, kuma kar a shagaltu da fira, ko tsintar duwatsun jifa

4. Idan Asuba tayi sai ayi Sallar Asuba, cikin Jam’i, kuma sai a zauna gari ya waye

5. A nan ne, Allah yayi horo ayita zikirin Allah, a Mash’airl Haram, yanzu Masallaci ne

Za’a tsaya wajen ayita zikiri har sai rana tayi kusa 6ullowa, ana addua tareda daga hannuwa

Sai a bar filin kafin fitowar rana zuwa Mina don jifa

UMRA A SAUKAKE

UMRA A SAUKAKE

Tun lokacin da ake Madina, ya kamata mutum ya fara shirin yin Umra.

Sheak Abdulhakeem Ahmad Ya’akub Gusau

image

Ta hanyar cire kumba da gashin Mara da gashin hamata da gashin baki, idan mutum yana bukatar yin hakan

Domin idan yayi Harma duka wannan ya haramta, har sai ya gama Umra

Idan kuma akaxo wajen Mikati, wajen Harma kenan sunan wajen Tan’eem

A nan mutum zaiyi wanka, idan yana bukatar sabulu to ya farayin na sabulun

Sai ya gama, sai yayi wankan Harma da Umra yadda ake wankan Janaba

Sai mutum ya shafawa jikinsa turare idan yanaso, amma ba a shafawa Harami

Sai kuma a cire suturarda akazo da ita, a daura Zane a kuma lulluba Zane, farare wato Harami kenan, da kuma takalmi silifa

Mace kuma zata sanya duk kayanda take bukata da zai rufe mata jiki kowace irin kalace

Amma bazata rufe fuskaba da tafuka, bazata sanya safar hannun ba

NIYAR UMRA:

Za’ayi Harma da Umra kamar haka,

Mutum yayi Alwala, idan lokacin Sallar Farillah ne yayi, idan lokacin ta bane sai yayi Nafila Raka’a biyu na Harma

A raka’ar Farko za a karanta fatiha da Qul’ya’ayyul kafirun, ta biyu fatiha da Qulhuwalla, kuma za’ayi Nafilar kowane lokacine

To idan kuma mace, tana jinin haila ko nifasi, bazatayi Sallar ba, farillah ko Nafila

Daga an Sallama, sai mutum yayi niya a zuciyarsa ya kuma fada da bakinsa

Yace: Nawaitul Umrata wa’ahramtu biha lilllahi Ta’ala, idan yace Rabbana takabbal minni ba komi

Ko yace Labaikkka Umratan. Daga nan sai ya fara yin talbiya itace:

Laibaikakkallahumma labbaik…..har zuwa Karshe, Namiji zai daga murya batareda wahalda kansa ba, mace kuwa ta sassauta murya

Za a cigaba da yin Talbiya tun daga sadda mota zata fara tafiya har sai anje Makka

Sai mutum yayi ido da ido da dakin ka’aba sannan sai   ya daina Talbiya don fara dawafin Umra

Kuma ana son yawaita Talbiya, duk lokacin da wani hali ya canza, idan angaji sai a huta, sai a Dora

DAWAFIN UMRA:

Idan Alhaji ya iso MAKKA, dazarar yaga dakin Ka’abah, sai shi dakatar da Talbiya

Sai ya tasamma Inda ake fara dawafi, dai dai Hajarul Assad

Akwai alama da zatasa mutum yagane saitin wajen shine tsanwan fitila daga sama(Green light)

1.Sai mutum yaje wajen dutsin Hajrul Aswad ya sunbunce shi, idan zai yiwu da sauki

Idan bai yiwu ba, sai mutum ya tabo da hannu sai ya sunbunci hannun

Idan bai yiwuba, sai mutum yayi nuni da hannu, yace:

Bismillahi Akbar, daga nan sai ya Fara dawafin

2 Sai mutum yayi Ildiba’i kafin ya fara, shine ya bude kafadarsa ta dama ya rufe ta hagu

Wannan ga namiji kawai bada mace ba, shima idan bai yi ba, ba komi akansa

3.Sai yatsaya daga dama ya sanya dakin Ka’aba hagunsa sai yace:

Allahumma imanan bika, watasdiqan bikitabika wawafa’an bi’ahdika wattiba’an bisunnati nabiyika

Idan bai iya wannan ba komi, sai ya fara dawafi kai tsaye

4. Namijin a zagayensa uku na Farko zaiyi sassaka, wato gudu_gudu, sauran zagaye hudu kuwa zaiyi tafiya

Amma waniya  banda mata, sukam zasuyi tafiya a cikin dukkan zagayen bakawai

Za’a cigaba da addu’oin duk da anka iya, hat agama

5. Idan ankawo daidai Rukunul yamaniy sai a karanta:

Rabbana atina fiddunya hasanatan wafil akhirati hasanatan wakina azabar nar, tsakaninsa da hajarul aswad

6.Kuma duk sanda yazo Rukunil yamani sai ya shafeshi yace, Bismillah Wallahu Akbar amma baza’a sumbunta ba

Duk akazo Hajarul aswad sai ayi nuni, ace Allahu Akbar.

Sai andawo Inda aka fara, sai ace daya, idan yadawo biyu, har zagaye bakwai

7. Idan an gama dawafin sai mutum ya rufe kafadarsa daya bude

Sai ya koma bayan Mukama Ibrahim yayi raka biyu na dawafi

Ba dole bane, sai ya matse mukam din ba, saboda cin kuson mutanen

Sai dai zai tsaya duk Inda yasamu wuri, a raka’ar Farko fatiha da Qulyah,, a tabiyu fatiha da Qulhuwa

8. Dagan nan a yafi shan ruwan zamzam ayi niyya kowace bukata akeso sai asha

Ana son a cika ciki, da ruwan kuma sai a zuba ruwan asaman kai

To daga nan an gama dawafi, sai dai idan ana cikin yi, mutum yayi kokanto

Sai a dauki adadin na kasa, misalin ana tunanin 4 ne ko 5

Sai a dauka Biyar ne, kuma Inda aka fara, nan ake gamawa

Ya halatta yin Magana ana dawafi, amma ta Alheri

Kuma ba’yin dawafi sai da alwala, don haka idan akayi takare sai an canza alwala

SA’AYI TSAKANIN SAFA DA MARWA

1.Daga nan sai a tasarwa dutsin safa, za’aga alamar zuwa wajen

Sai mutum yahau akan dutsin safa, sai a dubo wajen ka’abah, sai a daga hannuwa kamar za’ayi addua

Sai ace: Allahu Akbar 3, sai La’ilaha ilallahu wahdahu lasharika lahu, lahul mulk, walahul hamd, wahuwa alah kulli sha’ain Qadirun

La’ilaha Wahdahu Lasharikalahu anjaza wa’adah, wanasara abdah, wahazamal ahzaba wahdah

Idan mutum bai iya wannan ba, ko baiyi ba, ba komi

2.Sai mutum yayi addua duk abinda yake bukata, da larabci ko hausa

3. Daga nan sai ya tasowa Dutsin marwa, amma kafin ka iso, zaka cimma

Wani wuri, da ake kira (milaini akhdaraini) akwai fitila Kore(green light)

To a wannan za’ayi sassaka, sai an wuce sai a cigaba da tafiya

Wannan ya shafi namiji banda mata, duk akazo wajen haka za’ayi a zuwa ko dawowa

4. Daga Safa zuwa marwa, yana matsayin zuwa daya, dawowa matsayin daya, ba kamar dawafi ba

Don haka za’afara da safa agama da marwa, idan aka kare Inda aka fara anyi ragi ko kari

5. Za’a iya yin sa’ayi ko babu alwala, kuma idan anayi da alwala ta Kate za’a karasa kawai

6. Idan mutum ya gama, ya fara a safa ya kare a marwa, babu wata Nafila, bayan za’ayi

7. Daga nan namiji yayi aski, ko saisaye mace, kuwa ta kama gashinta daidai tsawon kan yatsa ta gutsire

8 Ya halatta yin magana ana sa’ayi amma ba afadar komi sai alheri

Kuma babu wata addua wadda dole sai ita, mutum abinda duk ya iya

Daga nan Umra ta kammala, sai acire Harami, duk abinda ya haramta yanzu ya hallata.

Sai kuma aikin Hajjin da za’a fara ranar 8, ga watan Hajj, zanyi bayani  insha Allahu.

Allah yasa ayi ibada karbabba, da fatar zaku tuna damu a cikin addu’o’inku

BAMU CHANCHANCI KOMAI BA DAGA GWAMNATI;A DAINA KASHEMU.

YAN GUDUN HIJIRA 100 AKA KASHE YAYIN DA MUTUM 8000 SUKA TSERO DAGA GIDAJEN SU A KARAMAR HUKUMAR ZURMI.

Daga Amag Abdoul.

Barayin Shanu naci gaba

image

da cin Karensu ba babbaka a cikin kauyukan Zurmi inda suke ci gaba da mamaye kauyuka tare da yiwa al-umma kisan gilla.

A daidai lokacin da shuwagabannin Nigeria ke murnar  kaddamar da layin dogo a jahar delta mukuma a Zamfara abun yasha banban muna jimami ne tare da rufe gawarwakin yan uwanmu da ake kashewa ba dare ba rana,tare da kokarin taya zamuyi mukai ga wadanda aka rabo da matsugunnan su hakazalika da kwana da zullumin samun sabbin hare-hare.

A jahata ta Zamfara munsan cewa bamuda wani amfani ga gwamnatin tarayya shiyasa bamu bukaci wani abun more rayuwa ba daga garesu saboda bamu chanchanci samun sa ba,babbar bukatar mu shine a daina kashemu.

A daina kashe mu
A daina kashe mu
A daina kashe mu

Shi muke nema kullum, inda ake nuna mana kullum rayuwar mutumin Zamfara batada wani amfani, idan kayi la’akari da yanda ake iya samar da dan sanda dubu talatin(30000) domin anaso ayi zabe; inda aka kasa samar mana da dan sanda dubu goma don kawo karshen matsalar tsaro.

Ana iya fitar da biliyoyan nairori don samar da motocin yakin zabe inda wlh a jahata ta Zamfa divisions mara adadi na yan sanda basu da motar sintiri.

Shin abun tambaya anan……….

Shin Zamfara ba gari bane ?
Mutanen Zamfara ba mutane Bane ?
Ba muda hakkin a kare rayukan mu ne ?

Allah ka zamo gatanmu a jahar Zamfara ka kawo mana karshen wannan musiba.

Ameen.http://jekadiyarzamfara

YAUCE RANAR YAKI DA SHAN MIYAGUN KWAYOYI A DUNIYA. Yau ce ranar yaki da shan miyagun kwayoyi a duniya Matasa da dama a sassan duniya na gurbata rayuwarsu saboda shan miyagun kwayoyi. Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don yaki da kwankwada da kuma safarar miyagun kwayoyin da ke sanya maye da kuma gurbata tunanin bil’adama. Bikin na yau na zuwa ne a dai dai lokacin da kasashe masu tasowa ke fama da yadda matasa ke rungumar mummunar dabi’ar shan wiwi da hodar iblis da magungunan da ke jirkita kwakwalarsu. Tun a ranar 7 ga watan Disamban shekarar 1987 Majalisar Dindin Duniya ta ayyana wannan rana ta 26 ga watan Yuni a matsayin ranar yaki da sha da kuma safarar kwayoyin. Taken ranar a bana shi ne, “sauraron yara da matasa shi ne mataki na farko wajen taimaka musu samun ci gaba a fannin kiwon lafiya da kuma samun kariya’’. A duk shekara ana samun tallafi daga al’umma da kungiyoyi daban-daban a sassan duniya don magance wannan matsala ta shaye-shaye. A shekarar 2016 majalisar ta gudanar da wani gagarumin taro kan illar kwayoyin, in da daga karshe ta fitar da wani mataki da mambobinta za su dauka wajen yaki da miyagun kwayoyin.