Yusuf Idris Gusau ya kara da cewa gwamnan ya kafa kwamitin amintattu ne inda bayan kammala aikinsu suka bayar da shawarwari ciki har da batun tsige masu sarautar guda biyun.

Ya kara da cewa kwamitin ya gano yadda masu garkuwa da jama’a ke amfani da sarakunan gargajiyar guda biyu wajen biyan kudin fansa

    A watan Yuni ne dai gwamnatin jihar ta Zamfara ta dakatar da sarakunan gargajiyar sakamakon bore da talakawa suka yi kan zargin mutanen biyu da alaka da masu satar jama’ar.

    Hakan ne kuma ya sa gwamnati kafa kwamitin amintattu karkashin jagorancin tsohon sifeto janar na ‘yan sanda, Muhammad Abubakar.

    Sai dai kawo yanzu BBC ba ta ji ta bakin mutanen da ake zargin ba kasancewar bayanai na nuna cewa tuni jami’an tsaro suka yi awon gaba da su zuwa birnin Abuja domin ci gaba da bincike.

    To amma a baya, BBC ta yi hira da wani dan uwan Sarkin na Maru, inda ya musanta zarge-zargen da ake yi wa dan uwan nasa.

    Ya ce bai kamata a zargi Sarki da alaka da bata gari ba, kasancewar Sarkin da kansa ya sha mika takardun da masu satar ke aike masa na yin barazana a gare shi amma jami’an tsaro ba su dauki mataki ba.

    An dai dade ana zargin sarakunan gargajiya da hannu a batun sata da garkuwa da jama’a da jihar ta dade tana fama