Yar Amuruka ta yo tattaki daga California zuwa Kano wajen saurayinta

A yanzu haka Mahaifiyar matashi mai suna Suleman ta amince Dan ta mai shejaru 23 ya bi Masoyiyarsa Mai shekaru 45 wacce tsuntsun soyayya ya dauko ta daga Amurka domin haduwa da masoyi ta da suka hadu a Instagram.


Baturiyar Birnin Carlifonia tazo daga Amurka har Garin Panshekara domin tabbatar da soyayyar ta ga matashi Suleman wanda suka Dade suna tsinkar fure online.

Yanzu Haka da zarar an kammala shirye shirye zata saka masoyin ta a gaba su wuce Amurka.

Fatima Suleman mahaifiyar matashin kuwa tace Bata da suka Dan haka ta bayar da greenlight ga masoyan.

Shima ango Suleman yace dama burinsa shine ya haifi ‘ya’ ya ruwa biyu barbarar yanyawa(half cast) gashi kuma ya tsinci dami a Kaala.

Ya kuma alkawarin zai dinga kawo ziyara Ana gaisawa.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment