Gov Masari ya amince da fara biyan sabon tsarin albashi na ₦30,000

“Gwamnatin jihar Katsina kalkashin jagorancin Mai girma Gwamnan jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari ta amince da biyan sabon tsarin albashi na naira dubu talatin (30k)”.


“Amincewa da sabon tsarin albashin ya biyo bayan tattaunawa ta tsawon kwana uku da akayi da Kungiyar Kwadago ta kasa reshen jihar Katsina da komitin da Gwamnatin jihar Katsina ta kafa kalkashin jagorancin sakataren Gwamnatin jihar Katsina Dr. Mustapha M. Inuwa wanda zai fidda yadda sabon tsarin albashin zai tabbata”.

“Aikin komitin ya fiddo gaskiyar abinda jihar Katsina take samu na kaso arzikin kasa da kuma kudaden shigar ta na cikin gida, ya bayyana yawan albashin da jihar Katsina keyi jiha da kananan hukumomi da malaman Makarantun firamare”.

“Daga karshe komitin ya tattauna da Kungiyar Kwadago an samu fahimtar juna an cimma matsaya, Gwamnatin jihar Katsina ta amince zata biya sabon tsarin albashin na (#30,000) ba tareda da sharadin rage ma’aikaci ko daya ba jiha da kananan hukumomi”.

“A cikin jawabin shugaban komitin sakataren Gwamnatin jihar Katsina Dr. Mustapha M. Inuwa ya bayyana cewa da yaddar Allah sabon tsarin albashin za’a fara biyan shi daga watan daya na shekarar nan da muke ciki ta 2020”.

“Daga karshe yayi godiya ga Kungiyar Kwadago kan yadda suke ba Gwamnati goyon baya da kuma yadda suka bada gudumuwa wajen tabbatar da an samu matsaya kan sabon tsarin albashin na (#30,000) ba tareda ankai ruwa rana ba”.

“Sakataren Gwamnatin har ila yau yayi godiya ga sauran yan komiti da suka bada gudumuwar su wajen tabbatar da samun matsaya tsakanin Gwamnati da Kungiyar Kwadago kuma aka samu nasara. Yayi addu’a Allah ya kara bada fahimtar juna tsakanin Kungiyar Kwadago da Gwamnatin jihar Katsina ya bamu lafiya da zama lafiya da karuwar arziki a jihar mu da kasar mu baki daya”.

“Yan komitin sun hada, shugaban ma’aikata na jihar Katsina (Head of Service) Alh. Idris Tune, shugaban Kungiyar Kwadago, babban akawunta na jihar Katsina (Accounter General) Alh. Malik Anas, Shugaban hukumar tara kudaden shiga ta jihar Katsina, Babban sakatare a ma’aikatar kudi ta jihar Katsina, mataimakin Babban Akawunta na jihar Katsina Alh. Sani Lawal BK, Kwamishinan ma’aikatar kulada kasafin kudi na jihar Katsina Hon. Faruk Jobe. Dadai sauransu”.

Report. Surajo Yandaki

Katsina State Apc Social Media Crew.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment