Gwamnatin Zamfara za ta hana yara yawon tallace-tallace a lokutan zuwa makaranta

Gwamnatin jihar Zamfara tace wata dokar dake gaban majalisar dokokin jihar zata hana yaran da suka kai shekarun zuwa makaranta yawon tallace-tallace yayin lokutan zuwa makaranta a jihar.

Gwamnan jihar Bello Matawalle, shine ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya karbi kyautar girmamawa akan jin dadin malaman makaranta a Enugu.

Kungiyar shugabannin makarantun firamare a Najeriya ce ta bashi kyautar.

Bello Matawalle, wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar ilimi bai daya a jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Maradun, yace gwamnati baza ta bar kowane yaro a bay aba, wajen kudirinta na tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ingattaccen ilimi matakin farko a kyauta kuma tilas.

A cewarsa, dokar tana kuma kokarin tallafawa gwamnati wajen ganin cewa dukkan yaran suke shekarun zuwa makaranta, suna zuwa makarantar domin samun ilimi a matakin farko.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

2 thoughts on “Gwamnatin Zamfara za ta hana yara yawon tallace-tallace a lokutan zuwa makaranta

Leave a comment