Dan Majalisa a Zamfara ya Sa Marayu 165 a Makaranta/Jekadiyar Zamfara

Dan majalisar wakilai daga jihar Zamfara, Alhaji Kabiru Maipalace ya samar wa da marayu da masu karamin karfi 165 guraben karatu don su samu ilimi.


Alhaji Kabiru Maipalace wanda shi ne yake wakiltar Gusau/Tsafe a majalisar tarayya ya fadi haka ne ta hanyar sakatarenshi, Mustafa Hassan.

Ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Nijeriya cewa, yaran masu karamin karfi ne da wadanda kuma suka kasa biyan kudin makaranta ba saboda talauci.

Dan majalisan ya ce, yaran sun samu shiga makarantu daban-daban a makarantun firamare mallakar gwamnati a Gusau da Tsafe.

“A Tsafe, mun sa yara 120 a makaranta, a Gusau kuma muka sama wa 45, sannan mun ba su kayan karatu.

“Ya ce wannan na daga cikin hadafinshi na rage yaran da basa zuwa makaranta a jihar,” inji shi.

Dan majalisan ya kara da cewa, ya nemo wa mutum 500 fom din fara karatu a manyan makarantun gaba da sakandire ga ‘yan mazabarsa da suke da burin ci gaba da karatu idan sun kammala sakandire.

“Mun sayo fom 50 daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Talatan Mafara, 40 daga Kwalejin ilimi ta Gusau, 30 daga Kwalejin Kiwon Lafiya a Tsafe.

“Sannan mun sayo 40 na Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Kaura-Namoda, 50 daga Kwalejin Ilimi na jihar Zamfara dake Maru, sai wasu 40 daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha, Kaduna da kuma 100 daga Jami’ar Tarayya dake Gusau.

“Mun sayo fom 50 na SBRS, Funtua wacce take karakashin kulawar Jami’ar Ahmadu Bello sai kuma 50 na Makarantar Sharar Fage ta Jami’ar Usman Danfodiyo dake Sakkwato.

“Za mu biya wa dukkan daliban da suka yi nasarar samun guraben karatun har su kamala karatunsu a wadannan makarantun,” inji shi.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment