Amarya ta haihu wata hudu da yin aurenta a Kano

Wata mai jego mai suna Maryam Bilal da madaurin auren ta Musa Khalil sun gurfana a gaban kotun majistratrate mai lamba 62, dake zaman ta a garin Minjibir, karkashin mai shari’ah Ibrahim Sarki Ibrahim, da tuhumar hada kai da aikata laifi da kuma cutarwa laifukan da suka saba da sashi na cashi’in da bakwai da kuma na dari uku da ashirin da biyu, na kundin tafikadda shari’ar musulunci na jihar Kano.

Wani mutum ne dai Aminu Ibrahim, ya yi karar su a ofishin ‘yan sanda na Minjibir cewar Musa Khalil din ya aura masa Maryam alhalin tana dauke da juna biyu, kuma watan ta hudu da kwana ashirin da takwas ta haihu.
Koda Dan sanda mai gabatar da kara sajan Kabiru Bashir ya karanta musu kunshin tuhumar da ake musu, sai suka musunta. A nan ne mai shari’ah Ibrahim Sarki Ibrahim, ya daga zaman zuwa ranar sha hudu ga wannan watan da mu ke ciki Dan cigaba.
Daga nan ne Lauyan da yake kare su ya roki kotun da ta sanya su a hannun beli. Kuma kotun ta amince da rokon ta kuma sanya su a hannun belin, bisa sharadin mutane biyu masu kamala su tsaya musu sannan kuma su bada hotunan su na passport guda biyu a kotun sannan kuma dan sandan kotun ya je ya gano gidajen su. In kuma wadanda akai belin suka tserewa shari’ah masu belin za su bada duba dari dari.
Kuma bayan an fito daga kotun Maryam din ta shaidawa wakilin mu Abubakar sabo cewa wani ne mai suna Sunusi Bala alale ya yi mata.
Shi ma madaurin auren na ta Musa Khalil ya magantu.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment