Gwamnatin Zamfara ta biya malamai 556 wadan da tsohuwar Gwam ta dauka har ta sauka ba ta biyasu albashi ba.

A Cigaba yunƙurin gwamnatin jahar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun, na tabbatar da walwala da jin daɗin al’ummar jaharsa. Tare da tabbatar da duk wani mai haƙƙi haƙƙinsa ya zo hannunsa.


Gwamnatin jahar Zamfara ta biya dukkanin ma’aikata 556 da tsohowar Gwamnatin Shehi ta ɗauka aiki. Amma har ta sauka ba ta taɓa biyansu albashi ba.

In dai ba a manta ba bayan hawan wannan Gwamnatin kan Karagar mulki, waɗannan matasan sunka kai kokensu ga Mai Daraja gwamna, a ranar da ya shiga gidan Rediyon jahar Zamfara wajen shirin zuwa-da-kai. Inda Gwamnan ya baiwa Malaman tabbacin cewa ya ga suna ɗaga masa kwali mai ɗauke da koken tsohowar Gwamnatin da ya gada ta ɗauke su aiki Amma ba a biyansu albashi, Wanda ya yi masu alƙawarin tabbatar da aikin nasu. Kuma nan take ya baiwa shugaban Ma’aikatan jahar Zamfara Alh. Kabir Balarabe Sardaunan Dan isa. Umurnin ya duba koken matasan. Bayan an tabbatar da cewa an ɗauke su aiki, akan ka’ida gwamnan ya tabbatar masu da cewa wannan watan na satumba za su shiga cikin waɗanda Gwamnatinsa ta biya albashi. Cikin ikon Allah wannan alƙawarin ya cika. Domin tuni, waɗannan matasa sunsamu albashinsu na farko a matsayin ma’aikata.

Idan dai ba a manta ko a watan da ya shuɗe gwamna Matawalle, ya tabbatar da matasa 1040 da tsohowar Gwamnatin da ya gada ta ɗauka aiki shekaru biyar, Amma ba ta taɓa biyansu albashi ba. Amma wannan Gwamnatin ta tabbatar da aikin Matasan.Tare da biyansu albashi nan take.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment